Babban Sallah: Coci A Kaduna Ta Raba Abinci Ga Musulmi Mabukata Da Marayu, Ta Yi Rabon Kudin 'Barka Da Sallah'

Babban Sallah: Coci A Kaduna Ta Raba Abinci Ga Musulmi Mabukata Da Marayu, Ta Yi Rabon Kudin 'Barka Da Sallah'

  • Cocin The Christ Evangelical and Life Intervention Fellowship Ministry a Kaduna ta raba abinci ga mabukata da marayu
  • Yohanna Buru, shugaban cocin ya kuma ce sun raba wa kananan yara kudin 'Barka da Sallah' kamar yadda suka saba fiye da shekaru 10
  • Buru ya ce cocinsa na wannan karamcin ne domin taimakawa marasa karfi su yi sallah cikin annashuwa da kuma kyautata zumunci tsakanin musulmi da kirista

Jihar Kaduna - Wani coci mai suna The Christ Evangelical and Life Intervention Fellowship Ministry ta raba abinci ga musulmi mabukata da marayu don murnar babban sallah.

Cocin ta kuma ce ta bada kyautan kudi na "Barka da Sallah" ga yara domin karfafa dankon zumunci tsakanin musulmi da kirista a jihar, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Trela Ta Markade Mutum 8 Da Ragunan Sallah Masu Yawa A Wani Mummunan Hatsari

Coci ta yi rabon abinci da sallah.
Babban Sallah: Coci A Kaduna Ta Raba Abinci Ga Musulmi Mabukata Da Marayu, Ta Yi Rabon Kudin 'Barka Da Sallah'. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin rabon kayan, Yohanna Buru, shugaban cocin ya ce abu ne mai muhimmanci a taimakawa musulmi mabukata su yi bikin sallah cikin murna.

Buru ya ce al'adar cocin ne raba wa mutane 600 - 700 abinci duk sallah - amma an kara adadin a bana saboda yawan mutane a yankunan sun karu.

Mafi yawancin wadanda aka bawa abinci, ya ce, masu bara ne a titi, wadanda mazajensu suka mutu, marayu da wasu yan sansanin gudun hijira.

Mun fi shekara 11 muna wannan al'adar

Malamin addinin ya kara da cewa, wannan al'adar da suka shafe kimanin shekaru 11 suna yi ne don habaka fahimtar juna, tattaunawa tsakanin addinai a Jihar Kaduna na nufin kawo zaman lafiya mai dorewa tsakanin musulmi da kirista.

Ya yi kira ga musulmi da kirista masu hannu da shuuni a kasar su rika taimakawa masu bukata da marayu, ya kara da cewa dukkan mu "yan uwan juna ne kuma dole mu tallafawa juna mu zauna lafiya".

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Babban Sallah: Biyayya Ga Koyarwar Addini Zai Magance Mafi Yawancin Matsalolin Mu, Buhari

A wani rahoton, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce idan yan Najeriya za su rika aiki da koyarwar addinai, da an warware mafi yawancin matsalolin da ke adabar al'umma, Nigerian Tribune ta rahoto.

A sakonsa na babban sallar ga musulmin kasar da sauran mutane a ranar Juma'a, Shugaba Buhari ya yi kira da al'umma su fifita kasa kan bukatun kansu kuma "su yi amfani da addini don zaburar da su son al'umma."

Asali: Legit.ng

Online view pixel