An Kama Ƴan Ta'addan Da Suka Sace Mahaifiyar Sanatan APC a Kano Da Kuma Kashe Jami'an Tsaro

An Kama Ƴan Ta'addan Da Suka Sace Mahaifiyar Sanatan APC a Kano Da Kuma Kashe Jami'an Tsaro

  • Yan sanda sun yi nasararkama wasu mutane biyu da ake zargi da kashe jami'in hukumar shige ta fice ta kasa da kuma garkuwa da mahaifiyar dan majalisar Kano
  • Wadanda aka kama din sune Safiyanu Muhammad dan shekara 35 a rugar makiyaya a Kano sai kuma Musa Idi dan shekara 40 a Laraba Gurgnya, Taura, Jihar Jigawa
  • Kwamshinan yan sandan Jihar Jigawa, Bashir Ahmad, ya jinjinawa dakarun yan sanda tare da yan bijilante da suka yi aikitare wurin kama wadanda ake zargin

Jigawa - Yan sanda a Jihar Jigawa sun kama mutane biyu da ake zargi da kashe jami'in hukumar shige da fice da kuma garkuwa da mahaifiyar sanatan APC mai wakiltar Kano ta tsakiya, Abdulkarim Abdulsalam.

Kakakin yan sandan jihar, Lawal Adam, ya ce yan sanda da yan bijilante ne suka gano wadanda ake zargin a wurare daban-daban a Kano da Jigawa, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Wani Matashi Ya Yi Barazanar Kashe Gwamnan APC

Wadanda ake zargi.
An Kama Ƴan Ta'addan Da Suka Sace Mahaifiyar Sanatan APC a Kano Da Kuma Kashe Jami'an Tsaro. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

A watan da ta gabata, Premium Times ta rahoto yadda yan ta'adda suka kashe jami'in shige da fice ɗaya suka raunata wasu biyu a karamar hukumar Birniwa, da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Kazalika, a watan Yuni, yan bindiga sun sace mahaifiyar Mr Abdulsalam a gidanta da ke karamar hukumar Ungogo a Kano.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daya baya an sako mahaifiyar dan majalisar bayan an biya kudin fansa.

Yadda aka kama wadanda ake zargin

Yan sandan sun ce an kama wadanda ake zargin ne a sansanin makiyaya a karamar hukumar Gabasawa na Jihar Kano, da kauyen Laraba Gurgunya a karamar hukumar Taura a Jigawa.

Mr Adam ya ce:

"A ranar 18/09/2022 tsakanin karfe 7 na yamma da 12.15 na rana, bayan samun bayanin sirri, tawagar yan sanda da yan bijilante daga hedkwata a Dutse da Ringim sun yi samame na musamman da ta yi sanadin kama hatsabiban yan ta'adda da ke adabar Jigawa da Kano.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: An Kama Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Sojan Bogi a Jihar Zamfara

"Yan sandan sun ce binciken farko ya nuna wadanda ake zargin ne suka kashe jami'an shige da fice a ranar 9 ga watan Agusta da kashe yan sanda a kauyen Kwalam a karamar hukumar Taura a ranar 23 ga watan Janairu yayin amsa kirar kai dauki."

Wadanda aka kama

Wadanda ake zargin da aka kama sune Safiyanu Muhammad, 35, mazaunin rugar makiyaya a Gabasawa Jihar Kano, da Musa Idi, 40, na rugar makiyaya ta Laraba Gurgunya, Taura, Jihar Jigawa.

Kwamishinan yan sanda na Jigawa, Bashir Ahmad, ya yaba da kokarin jami'an da yan bijilante bisa aiki mai kyau da suka yi.

Yadda Na Ke Kai Wa Yan Ta'adda Kayan Abinci Da Kudin Fansa A Zamfara - Wanda Ake Zargi

A wani rahoton, Alhassan Lawali, wani da ake zargi dan leken asirin yan bindigan Zamfara ne ya bayyana yadda ya rika kai wa yan bindiga kudin fansa da kayan abinci.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Bayyana Wa Yan Sanda Yadda Ya Ke Amfani Da Farin Takarda Wurin Damfara Masu POS

Mohammed Shehu, kakakin yan sandan jihar Zamfara, ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel