Ina danasani: Budurwa Mai Da Al’aurar Namiji Da Mace Ta Koka Bayan Ta Cire Daya A Bidiyo

Ina danasani: Budurwa Mai Da Al’aurar Namiji Da Mace Ta Koka Bayan Ta Cire Daya A Bidiyo

  • Wata kyakkyawar budurwa ta bayyana damuwarta a TikTok bayan ta cire daya daga cikin al’aurarta
  • Matashiyar mai suna @Ifyberry1 a TikTok ta yi ikirarin cewa an haifeta da al’aurar namiji da mace
  • Ify ta ce a karshe ta yanke shawarar cire daya daga ciki amma bayan ta dauki matakin, sai tana danasanin hukuncin da ta dauka

Wata matashiya yar Najeriya ta tuna halin da ta shiga bayan ta cire daya daga cikin al’urarta guda biyu.

Budurwar mai suna @ifyberry1 a TikTok ta ce an haifeta a matsayin mata-maza wato tana dauke da al’aurar namiji da mace.

Budurwa
Ina danasani: Budurwar Dake Da Al’aurar Namiji Da Mace Ta Koka Bayan Ta Cire Daya A Bidiyo Hoto: @ifyberry1
Asali: UGC

A kwanaki, sai ta yanke shawarar cire daya daga cikin al’aurar amma nan take ta fara danasanin matakin da ta dauka bayan aikin gama ya gama.

Ify ta yi karin haske a wallafar tata cewa ta cire al’aurar namiji sai ta fara jin babu dadi sannan ta fara kewar yanayinta na baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta bata son rayuwar ‘ya mace kuma tana muradin komawa mata-mazanta.

Kalamanta:

“Nayi kewar kasancewa mata-maza. Na yi danasanin cire al’aura daya. Ta yaya zan saba da wannan sabuwar rayuwa? Wannan rayuwar ta ‘ya mace ba nawa bane.”

Jama’a sun yi martani

@onyekachukwu383 ta ce:

“Na fahimci damuwarki bebi ki ziyarceni kai tsaye don mu fita yawo.”

@jihadfardbilal.bey ya rubuta:

“Za ki fita daga wannan yanayin kawai ki tuna cewa ke din ce dai.”

@estherchiugo ta ce:

“Je ki mayar da shi kada ki wahalar da mu.”

@cumybtc ta ce:

“Shirme kawai, baki ma san abun da kike so ba.”

Kalli bidiyon a kasa:

"Zan Iya Yiwa Mace Ciki": 'Yar Najeriya Mai Al'aurar Namiji da Mace Na Neman Wanda Zai Aureta

A wani labarin, wata yar Najeriya ta tada kura a kafafen yada zumunta bayan bayyana cewa ita mutum ce mai al'aurar mata da na maza.

A bidiyon TikTok din da ta saki, ta bayyana cewa haka iyayenta suka haifeta.

A wani bidiyo da ta saki daga baya, ta bayyana cewa duk wanda ke son aurenta ya sani cewa ba ta jinin al'ada kuma za ta iya dirkawa wata mace ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel