"Zan Iya Yiwa Mace Ciki": 'Yar Najeriya Mai Al'aurar Namiji da Mace Na Neman Wanda Zai Aureta

"Zan Iya Yiwa Mace Ciki": 'Yar Najeriya Mai Al'aurar Namiji da Mace Na Neman Wanda Zai Aureta

  • Wata yar Najeriya da aka haifa da al'aurar namiji da na mace ta bayyanawa duniya halin da take ciki
  • Matar wacce tace tana da 'diya mace yanzu haka ta ce fa amma a sani bata jinin al'ada
  • Yayinda ta bayyana cewa tana neman masoyin aure, ta bayyana cewa tana iya yiwa mace cicki

Wata yar Najeriya ta tada kura a kafafen yada zumunta bayan bayyana cewa ita mutum ce mai al'aurar mata da na maza.

A bidiyon TikTok din da ta saki, ta bayyana cewa haka iyayenta suka haifeta.

Hamed
"Zan Iya Yiwa Mace Ciki": 'Yar Najeriya Mai Al'aurar Namiji da Mace Na Neman Wanda Zai Aureta Hoto: TikTok/@queenofpeople5
Asali: UGC

A wani bidiyo da ta saki daga baya, ta bayyana cewa duk wanda ke son aurenta ya sani cewa ba ta jinin al'ada kuma za ta iya dirkawa wata mace ciki.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

Ta bayyana cewa tana da diya mace kuma ita ta yiwa matar da ta haifi yarinyar ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel