An Jefar da Karar da Abduljabbar Kabara Ya Kai Gwamnati, An Ci Shi Tarar N100, 000

An Jefar da Karar da Abduljabbar Kabara Ya Kai Gwamnati, An Ci Shi Tarar N100, 000

  • Kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta yi zama domin sauraron karar Sheikh Abduljabbar Kabara
  • Alkali Emeka Nwite yace Lauyan da ya tsayawa Abduljabbar Kabara ya yi kokarin raina masa hankali
  • Kotu ta fahimci Shehu Dalhatu ya shigar da makamancin karar da ya kawo a gaban wani Alkalin
  • A karshen zaman da aka yi, kotu ta bukaci Lauyan da ya tsayawa malamin ya biya tarar N100, 000

Abuja - A ranar Litinin, 19 ga watan Satumba 2022, babban kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da karar da Sheikh Abduljabbar Kabara ya shigar.

Sheikh Abduljabbar Kabara yana karar gwamnatin jihar Kano bisa zargin tauye masa hakki a matsayin ‘dan kasa, Daily Nigerian tace an yi watsi da karar.

Mai shari’a Emeka Nwite ya saurari wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1201/2022 a dazu, inda ya zartar da hukuncin cewa mai karar na wasa da shari’a.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Dan China Ya Yaudari Ummita a Kan Shiga Musulunci inji Babbar Kawar Ummita

Emeka Nwite yace Abduljabbar Kabara ya shigar da irin wannan kara a wata kotu da ke Kano, don haka babu dalilin sake kawo ta a makamancin kotun.

Alkali ya yi Allah-wadai da Lauya

Alkalin yake cewa Lauyan malamin watau Shehu Dalhatu, ya yi kokarin nuna masa sabuwar kara dabam ya kawo, ba irin wanda ake sauraro a Kano ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A dalilin wannan, mai shari’a Nwite ya yi kaca-kaca da Dalhatu saboda wasa da kuliya, yace abin da wannan Lauya ya aikata abin ayi Allah wadai ne.

Abduljabbar Kabara
Sheikh Abduljabbar Kabara Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN tace Lauyan Sheikh Kabara ya maka babban kotun shari’a ta Kofar Kudu da gwamnatin Kano a kotun na Abuja.

Shehu Dalhatu yana tuhumar gwamnati da kotu da tauyewa Kabara hakkin da dokar kasa ta ba shi. Masu kare karar sun roki Alkali ya yi fatali da shari'ar nan.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamna Ganduje Ya Ware biliyan N1.2 Don Ayyukan Hanyoyi 42

Lauyoyin da suka tsayawa wadanda ake tuhuma sun sanar da kotun tarayyar na Abuja an shigar da sak wannan kara a Kano da lamba FHC/KN/CS/185/2022.

Korafin Abdussalam Saleh

Rahoton da muka samu yace Lauyan da ke bada kariya ga gwamnati ya nemi a soke karar domin kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron laifin shari’ar Musulunci.

Bugu da kari, an zargi Lauyan shehin da cewa bai tattaro bayanin zaman da aka yi a kotun shari’a na Kano ba domin Alkali ya iya yin hukunci da kyau a Abuja.

An ci Kabara tarar N100, 000

Daily Trust ta rahoto Alkalin ya ci mai karar tarar N100, 000. Lauyan da ya kawo karar, Shehu Dalhatu shi ne zai biya wannan kudi ga gwamnatin jihar Kano.

A cikin fushi, mai shari'a yace babu dalilin raba kara daya a kotu biyu, yayi kaca-kaca da Lauyan, yace kotun koli ta taba hukunta wasu KLauyoyi a kan irin haka.

Kara karanta wannan

Al-Mustapha Ya Fashe Da Kuka Ya Zubar Da Hawaye Kan Rashin Tsaro A Najeriya

Yadda aka fara shari'a

Kwanakin baya mun kawo maku rahoto, Abduljabbar Nasiru Kabara ya dauki hayar Lauya, ya kai karar Gwamnatin Abdullahi Ganduje da kotun shari’ar Kano.

Dalhatu Shehu-Usman ya tsayawa Sheikh Kabara, yana neman a tsaida shari’ar da ake yi da Malamin, yace ba ayi masa adalci ba da ake ta tsare shi tun bara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel