Cikin Sa'o'i 8 Kacal, Dangote ya Tafka Asarar N9.42b, Arzikinsa Ya Koma Kamar na 2021
- Arzikin Aliko Dangote ya ragu inda yayi kasa fiye da misali kuma alamu na nuna cewa ba dole ya farfado da wuri
- Arzikin mashahurin 'dan kasuwan ya kai kololuwa a watan Yuni kuma yana dab da shiga cikin jerin biloniyoyi 50 na duniya
- Amma Dangote ya tafka gagagrumar asara inda makuden kudi har N9.42 biliyan suka zuge daga dukiyarsa cikin sa'o'i takwas kacal
Hamshakin mai arzikin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya tafka asara inda dukiyarsa tayi kasa wanda bata taba yi ba a cikin watanni 12, kuma a halin yanzu dukiyarsa $18.8 biliyan ce cif.
Wannan ya faru ne bayan da $22.0 miliyan na dukiyarsa suka lalace a cikin kasuwanci cikin sa'o'i takwas kacal a ranar Laraba, 14 ga watan Satumban 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan Satumban shekarar da ta gabata, dukiyar Aliko Dangote tana $18 biliyan ne.
Kamar yadda rahoton Bloomberg na biloniyoyi ya bayyana, shugaban kamfanonin Dangote ya tafka asarar $246 miliyan wanda yayi daidai da N105.43 biliyan tun daga farkon shekarar nan.
Wannan asarar da Dangote ya tafka tana nufin ya sauka a cikin jerin biloniyoyin duniya zuwa na 78 a maimakon na 60 da yake a watan Yunin 2022.
Bayani kan arzikin Dangote
Masana'antun Dangote dukkansu suna karkashin hamshakin 'dan kasuwa kuma mai arzikin Afrika ne.
Kamfanin simintin dangote sun kasance masu samar da siminti mafi yawa a Afrika kuma mallakin 'dan Kano ne mazaunin Legas wanda ya zamo shine ginshikin arzikinsa a yanzu.
Binciken da Legit.ng ta gudanar ya bayyana cewa, faduwar arzikinsa tana da alaka da rage kima da kamfanin simintinsa yayi.
Tun a farkon shekarar 2022, darajar kamfanin ta fadi zuwa N2.17 tiriliyan daga N4.86 tiriliyan a karashen watan Janairun 2022.
Manyan masu arziki 10 a duniya a kiyasin ranar 14 ga watan Satumban 2022
Elon Musk $264bn
Jeff Bezos $152bn
Gautam Adani $145bn
Bernard Arnault $135bn
Bill Gates $114bn
Warren Buffett $97.1bn
Larry Page $96.5bn
Sergey Brin $92.3bn
Mukesh Ambani $92.2bn
Larry Ellison $92.0B -$2.91bn
Sunayen biloniyoyi 87 na duniya: Dangote ya fi kowa kudi a Afrika, Elon Musk ya ninka shi sau 15
A wani labari na daban, mujallar Forbes ta saki jerin sunayen wadanda suka fi kowa dukiya a duniya, wanda takwas daga cikin goma na farko 'yan kasar Amurka ne, sai daya daga Faransa da kuma daya daga Indiya.
Har yanzu, Amurka ce ke mulkar duniya, wacce ke da biloniyoyi 735 da jimillar dukiyar $4.7 tiriliyan, duk da Elon Musk, wanda yazo na farko a jerin sunayen biloniyoyin duniya a karo na farko sama da Jeff Bezos.
Asali: Legit.ng