Ana Tsaka da Rikicin Cikin Gida, Ayu Ya Mika Mulkin Jam'iyya Hannun Mataimakinsa, Ya Bayyana Dalilinsa

Ana Tsaka da Rikicin Cikin Gida, Ayu Ya Mika Mulkin Jam'iyya Hannun Mataimakinsa, Ya Bayyana Dalilinsa

  • Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, ya mika ragamar mulkin jam'iyyar hannun mataimakinsa ana tsaka da rikicin son ya sauka
  • Kamar yadda hadimin Ayu a fannin yada labarai ya sanar, Ayu zai shilla Turai ne duk da bai bayyana wacce kasa ba kuma a wanne dalili
  • Kafin ranar 28 ga Satumba ake sa ran kaddamar da kwamitin kamfen din jam'iyyar, hakan na nufin babu Ayu a wurin tunda baya kasar

Duk da rikicin cikin gida na jam'iyyar PDP da ya ki ci balle cinyewa, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, ya mika ragamar jam'iyyar hannun mataimakinsa na arewa, Umar Iliya Damagum.

Mai bai wa Ayu shawara na musamman a fannin yada labarai da sadarwa, Simon Imobo-Tswam, a yammacin Talata ya sanar da cewa Ayu zai bar kasar nan har zuwa karshen wannan watan.

Kara karanta wannan

Rikicin Ya Barke A NNPP, An Rushe Shugabancin Jam'iyya Na Wata Jiha

Iyorchia Ayu
Ana Tsaka da Rikicin Cikin Gida, Ayu Ya Mika Mulkin Jam'iyya Hannun Mataimakinsa, Ya Bayyana Dalilinsa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa, Ayu zai dire a Turai ne amma bai bayyana wacce kasa ba kuma mene ne dalilin tafiyarsa.

Jam'iyyar PDP zata bayyana kwamitin kamfenta din ta kafin ranar 28 ga watan Satumban 2022 wanda za a fara yakin neman zabe gadan-gadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na nufin cewa ba dole Ayu ya kasance a kasar nan ba yayin da za a sanar da kwamitin kamfen din kuma har a fara gangamin neman zaben.

Jam'iyyar PDP dai ta cika da rikicin cikin gida tun bayan da Atiku Abubakar yayi nasarar yin caraf da tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar kuma ya zabi gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin tafiyarsa a maimakon Gwamna Wike na jihar Ribas.

Wike da 'yan tsaginsa sun dinga yaki da Ayu da Atiku inda suke jaddada cewa dole shugaban jam'iyyar na kasa yayi murabus don 'dan kudancin kasar nan ya karba ragamar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Akwai Aiki A gaba: Sanatan PDP Ya Bayyana Abun Da Zai Faru Idan Ayu Ya Yi Murabus

Duk Masu Shirya Yadda Zasu Halakani, Su Zasu Fara Mutuwa, Wike

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ana barazanar da ake masa sakamakon rikicin cikin gida na PDP inda yace masu son kashe shi zasu mutu kafin su kai ga halaka shi.

Gwamnan yayin jaddada cewa tun 1999 jihar na bada goyon baya a fannin kuri'u da kudi fiye da sauran jihohi. A cewarsa:

"Ya isa haka kan yadda ake amfani da watsi da 'yan PDP."

Asali: Legit.ng

Online view pixel