Za a Gurfanar da Mamu a Gaban Kotu, DSS ta Haramtawa Lauyoyi da 'Yan Uwansa Ganinsa

Za a Gurfanar da Mamu a Gaban Kotu, DSS ta Haramtawa Lauyoyi da 'Yan Uwansa Ganinsa

  • Ta yuwu hukumar tsaron farin kaya, DSS, ta gurfanar da Malam Tukur Mamu, mai sasanci da 'yan bindiga a gaban kuliya ranar Litinin
  • Kamar yadda majiya daga iyalansa ta sanar, jami'an DSS a hedkwatarsu ta Abuja sun hana Mamu ganawa da lauyoyin da suka je ganinsa
  • Har ila yau, wasu daga cikin iyalansa a cikin makon da ya gabata sun kai masa ziyara amma aka hana su ganinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Alamun da suka bayyana a cikin kwanakin karshen makon nan shi ne, ta yuwu a gurfanar da mai sasanci da 'yan bindiga, Tukur Mamu, a gaban kotu a Abuja ranar Litinin.

Hukumar tsaron farin kaya wacce yake hannunta, ta hana lauyoyi da iyalai ganin mamallakin jaridar Desert Herald din wanda jami'ai suka yi ram da shi a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Iyalan Tukur Mamu Wanke Shi Daga Zargi, Sun Bayyana Wanda Ke Da Kayan Sojojin Da DSS Ta Gano A Gidansa

A ranar Talata aka cafke Mamu da matasan biyu tare da 'ya'yansa maza biyu a kasar Misra yayin da suke hanyarsu ta zuwa Umra a kasar Saudi Arabia.

Malam Tukur Mamu
Za a Gurfanar da Mamu a Gaban Kotu, DSS ta Haramtawa Lauyoyi da 'Yan Uwansa Ganinsa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan an tsaresa na tsawon sa'o'i 24 a Cairo, an dawo da shi Najeriya inda jami'an DSS suka yi ram da shi a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu dake Kano,.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta rahoto cewa, wata majiya daga iyalansa sun sanar da cewa tawagar lauyoyi karkashin jagorancin Barista Sani Ningi ta je hedkwatar DSS ta Abuja domin ganawa da Tukur Mamu amma aka hana su ganinsa.

Hakazalika, wasu daga cikin iyalansa sun yi wannan yunkurin amma aka hana su ganinsa.

Jami'an hukumar DSS a ranar Alhamis 8 ga Satumban 2022 wurin karfe 12:30 na dare sun kai samame gidan Mamu da ofisoshinsa a Kaduna inda suka yi awon gaba da wayoyi, kwamfuyutoci, tsabar kudi da sauransu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: DSS Ta Kama Mahaifin Matar Tukur Mamu A Yayin Da Ake Fadada Bincike

Jami'an DSS sun ce sun samu abubuwan tambaya kamar kudi mai yawa na kasashen ketare tare da kayan sojoji a gidansa yayin samamen.

Jami'an DSS Sun Dira Gidan Tukur Mamu, Sun Kwashe Kwamfuyutoci da Takardu

A wani labari na daban, jami'an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, sun kutsa gidan Tukur Mamu, mai sasanci tsakanin 'yan bindiga da iyalan wadanda suka sace a Kaduna a sa'o'in farko na ranar Alhamis.

Jami'an sun bayyana a kusan motoci 20 wanda ganau ne ya tabbatar da hakan ga Daily Trust.

"Sun bincike gidan tare da yin awon gaba da takardu, wayoyi da kwamfuyutoci."

- Ganau ya tabbatar da hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel