Kwararrun Likitoci 500 ne suka bar Najeriya Cikin Shekaru Biyu, inji Kungiyar Likitoci

Kwararrun Likitoci 500 ne suka bar Najeriya Cikin Shekaru Biyu, inji Kungiyar Likitoci

  • Kungiyar kwararrun likitoci ta Najeriya ta koka ga yadda gwamnati ke yiwa likitoci rikon sakainar kashi
  • Akalla likitoci 500 ne suka bar Najeriya a cikin kasa da shekaru biyu domin neman aiki a kasar waje
  • Ana yawan samun rikici tsakanin ma'aikata da gwamnatin Najeriya, lamarin da ke kaiwa ga yajin aiki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Benin - Kungiyar kwararrun likitoci ta Najeriya ta shaida cewa, akalla kwararrun likotoci 500 ne suka fice daga Najeriya domin kama aiki a wasu kasashen waje.

Kungiyar ta ce, likitocin da yawansu ma'aikatan gwamnatin jihohi ne da na tarayya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Dr Victor Makanjuola ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Benin yayin da yake amsa tambayoyi kan taron kungiyar na shekara-shekara da aka gudanar.

Yaddaa likitocin Najeriya ke barin kasar
Kwararrun Likitoci 500 ne suka bar Najeriya Cikin Shekaru Biyu, inji Kungiyar Likitoci | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ta'allaka laifin ficewar likitoci daga Najeriya ga gwamnatin kasar, inda yace sam gwamnati bata ba da cikakkiyar kulawa ga bangaren lafiya da kuma kula da jin dadin ma'aikata har ma da mutunta su.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Kotu Bayan Sun Gaza Cimma Matsaya A Tattaunawarsu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake bayyana dalili, ya ce neman cikakken kwanciyar hankali dadin rai ke sa liktocin ke tsallakewa zuwa kasashen da zasu sami tsarin aiki mai dadi.

A cewarsa:

“A shekaru biyu da suka gabata, sama da kwararrun likitoci 500 ne suka bar aiki a asibitocin gwamnatoci don komawa aiki a kasashen waje. Dukkan asibitoci gwamnati na karkashin kulawar kwararrun liktoci ne, wanda shine tsari a ko'ina a duniya.
"A yanzu, mun yi rashin kwararrun liktoci 500 a cikin shekaru biyu kacal kuma mun gano cewa wadanda ka iya tafiya matasa ne masu jini a jika."

Mafita ga wannan matsala da ta shafi fannin lafiya a Najeriya

Daga mafitar da ya bayar, Dr Victor ya ce, akwai bukatar hana liktocin da suke tsakanin shekaru barin kasar don horar da masu tasowa a nan gaba, LindaIkeji'sBlog ya tattaro.

Kara karanta wannan

Elizabeth II: Shugaba A Afirka Ya Ayyana Zaman Makoki Na Kwana 3 A Kasarsa Don Jimamin Rasuwar Sarauniyar Birtaniya

Ya koka da cewa, rashin yin hakan zai sa ake asarar likitoci masu jini a jika yayin da masu yawan shekaru kuma za su yi ritaya, lamarin da zai iya dagula fannin lafiya a Najeriya.

Hakazalika, ya bukaci gwamnati ta kara wa'adin ritaya ga likitoci daga shekaru 60 zuwa 70.

A bangare guda, ya koka da yadda gwamnati ke yiwa ma'aikatan lafiya rikon sakainar kashi, inda yace kamata ya yi gwamnati ta warwaree matsalolin ma'aikata cikin makwanni biyu.

Daga karshe ya shaida cewa, kungiyar ba za ta iya yin komai ba idan ma'aikatan da ke karkashinta suka tunzura suka shiga yajin aiki.

Yadda Yajin Aikin ASUU Ya Maida Dalibin Likitanci Mai Siyar da Abinci a Jihar Sokoto

A wani labarin, Usman Abubakar-Rimi, wani dalibin ajin karshe a fannin likitanci a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (UDUS) ya bayyana yadda ya fara sana'ar abinci a kan saboda tsawaitar yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

Kara karanta wannan

Yakar talauci: Gwamna ya ba da umarnin a mayarwa mahajjata wani adadi na kudin da suka biyu na hajji

Idan baku manta ba, ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun bana, inda ta kora dalibai gidan iyayensu tare da maida su 'yan zaman kashe wando, Daily Trust ta ruwaito.

Abubakar-Rimi ya ce zama bai kama shi ba, domin dole ya nemi abin yi domin kashe lokaci da kuma iya daukar nauyin rayuwa da dai sauran abubuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel