Gwamna Matawalle Ya Umarci a Mayarwa Mahajjata Bana N50,000 Don Rage Musu Radadin Talauci

Gwamna Matawalle Ya Umarci a Mayarwa Mahajjata Bana N50,000 Don Rage Musu Radadin Talauci

  • Gwamntin jihar Zamfara za ta mayarwa mahajjatan da suka yi hajjjin 2022 N50,000 domin rage radadin talauci
  • Najeriya na fama da matsin tattalin arziki, lamarin dake kara sanya 'yan kasar cikin matsi da kuncin rayuwa
  • Gwamnan ya kuma kira 'yan jihar da su ba hukumomin tsaro hadin kai domin warware matsalolin tsaro

Jihar Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci a mayarwa mahajjata 1,318 na hajjin 2022 N50,000 kowanensu a fadin jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wannan batu na matawalle na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinansa na yada labarai, Ibrahim Dosara ya fitar a ranar Laraba 7 ga watan Satumba a Gusau, babban birnin jihar.

Kwamishina Dosara ya shaida cewa hakan na daga cikin yunkurin ba da agaji da gwamnatin jihar ke yi domin rage matsin tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna a Arewa ya kori dukkan kwamishinoninsa a yau Laraba

Matawalle zai mayarwa mahajjata kudin da sauka kashe
Gwamna Matawalle ya umarci a ba mahajjata N50,000 don rage musu radadin talauci | Hoto: dailynigeruan.com
Asali: UGC

Hakazalika, ya kuma umarci ofishin alhazai na jihar da ya gaggauta wannan rabon kudi ga mahajjatan da suka sauke farali.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, hukumar ta alhazai ta tsara fara ba da kudaden ne a ranar Litinin 12 ga watan Satumba a kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomi 14 na jihar.

A cewar sanarwar kwamishinan:

“Saboda haka, ana shawartar mahajjatan da su je kananan hukumominsu, inda suka biya kudin kujerar hajji domin karbar N50,000 daga ranar 12 ga watan Satumba."

Dosara ya kuma bayyana cewa gwamna Matawalle ya ba da tabbacin kara kokarin gwamnati wajen inganta tsaro, samar da ababen more rayuwa da dai sauran romin dimokuradiyya a jihar.

Daga karshe, gwamnati na kuma kira ga jama'ar jihar da su ci gaba da ba hukumomi hadin kai don warware batutuwan tsaro a fadin jihar, Gazzete ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Ya Koma Jami'ar Da Yayi Karatu, Yace Su Bashi Kudinsa Su Karbi Kwalinsu

Jerin adadin kujerun Hajji da kowace jiha ta samu a Najeriya, wasu jihohi hudu ba su da ko ɗaya

A wani labarin, hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) ta ce jihohin Ribas, Bayelsa, Akwa Ibom da Imo ba su samu kujera ko ɗaya ba a wannan shekarar.

Daily Trust ta ruwaito cewa kuɗin aikin Hajji na bana 2022 ka iya ƙaruwa da sama da kashi 50, a cewar hukumar NAHCON.

A shekarar 2019, Mahajjata sun biya miliyan N1.5m, bisa haka duk mutanen da suka aje kuɗin su tun shekarar 2020, za su ƙara akalla Miliyan ɗaya a sama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel