Gwamnan Legas Ya Nada Sabon Kwamishinan Tsare-Tsare da Cigaban Birane

Gwamnan Legas Ya Nada Sabon Kwamishinan Tsare-Tsare da Cigaban Birane

  • Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya naɗa Bamgbose-Martins a matsayin sabon kwamishinan tsare-tsare ta raya birane
  • Tsohon kwamishina, Dakta Idris Salako, ya yi murabus daga kujerarsa ne bayan wani Bene mai hawa Bakwai ya danne mutane
  • Rushewar Benen ya jawo akalla mutane shida suka rasa rayuwarsu kuma ba shi ne karo na farko ba a Legas

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya naɗa Injiniya Omotayo Bamgbose-Martins, a matsayin sabon kwamishinan tsare-tsaren Fili da raya birane.

Vanguard ta ruwaito cewa Mista Bamgbose-Martins zai maye gurbin Dakta Idris Salako, wanda ya yi murabus daga kujerar ranar Litinin da ta gabata.

Injiniya Bamgbose-Martins.
Gwamnan Legas Ya Nada Sabon Kwamishinan Tsare-Tsare da Cigaban Birane Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Tsohon kwamishinan ya aje aikinsa ne awanni 24 bayan Ginin Bene mai hawa Bakwai ya rufta kan mutane a jerin gidajen Oniru Estate, yankin Victoria Island, jihar Legas, inda aka rasa rayuka shida.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan Arewa Ya Naɗa Mutum Bakwai a Wasu Manyan Kujeru

Legit.ng Hausa ta gano cewa gabanin wannan naɗin da aka masa, Bamgbose-Martins, ya kasance kwamishinan ayyuka na musamman.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamshinan yaɗa labarai da dabaru na jihar Legas, Gbenga Omotoso, shi ne ya bayyana sabon cigaban ranar Laraba a birnin Ikeja, Premium Times ta ruwaito.

A cewar Mista Omotoso:

"Muna mai sanar da ɗaukacin al'umma cewa mai girma gwamna Babajide Sanwo-Olu, ya naɗa Injiniya Omotayo Bamgbose-Martins, a matsayin sabon kwamishinan tsare-tsaren fili da raya birane."
"Zai maye gurbin Dakta Idris Salako, wanda ya yi murabus daga kan kujerarsa a baya-bayan nan."
"Sabon kwamishinan da aka naɗa ya zo da ɗumbin kwarewa kasancewarsa tsohon kwamishinan ayyuka na musamman, mutum mai fasaha da zaku iya dogara da shi."

Gwamnan Osun zai ɗauki sabbin Malamai

A wani labarin kuma Bayan Shan Kaye a Zaɓe, Gwamna APC Zai Ɗauki Sabbin Ma'aikata a Jihar Osun

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kungiyar Kwallon Chelsea Ta Sallami Kocinta, Thomas Tuchel

Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya amince da ƙara ɗaukar sabbin malamai dubu ɗaya da ɗari biyar a sassan jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai, Funke Egbemode, yace matakin ɗaukar malaman zai cike gurbin dake tsakanin Malamai da ɗalibai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel