Kungiyar Kwallon Chelsea Ta Sallami Kocinta, Thomas Tuchel

Kungiyar Kwallon Chelsea Ta Sallami Kocinta, Thomas Tuchel

Kungiyar Kwallon Chelsea a kasar Ingila ta sallami Kocinta Thomas Tuchel, bayan wasanni bakwai kacal sabuwar kaka sakamakon kashin da ta sha hannun Dynami Zagreb a gasar zakarun Turai.

Chelsea ta jawabin da ta fitar ranar Laraba, tace ta sallami kocinta dan kasar Jamus duk da nasarar da yayi na lashe kofin zakarun turai da na duniya a 2021.

A cewar kungiyar:

"A madadin kowa a kungiyar kwallon Chelsea FC, muna son mika godiya ga Thomas da abokan aikinsa da kuma dukkan kokarin da sukayi yayin zamansu a kungiyar."

"Ko shakka babu Thomas ya shiga tarihin Chelsea bayan lashe kofin zakarun Turai, Super Cup da Club World Cup."

A sabuwar Kakar kwallom firimiya, Chelsea tayi nasara a wasanni uku, ta fadi biyu kuma tayi kunnen jaki 1.

Kara karanta wannan

Wani batu ya taso, Tinubu da Shettima za su kai ziyara sakaeriyar APC, an girke jami'an tsaro

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Online view pixel