Bayan Shan Kaye a Zaɓe, Gwamna APC Zai Ɗauki Sabbin Ma'aikata a Jihar Osun

Bayan Shan Kaye a Zaɓe, Gwamna APC Zai Ɗauki Sabbin Ma'aikata a Jihar Osun

  • Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya amince da ƙara ɗaukar sabbin malamai dubu ɗaya da ɗari biyar a sassan jihar
  • Kwamishinan yaɗa labarai, Funke Egbemode, yace matakin ɗaukar malaman zai cike gurbin dake tsakanin Malamai da ɗalibai
  • Sai dai zaɓaɓɓen gwamna mai jiran gado, Sanata Adeleke, ya ce wannan wata manaƙisa ce da nufin talauta jihar Osun

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Osun - Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya amince da ƙara ɗaukar sabbin malaman makaranta 1,500 da nufin cike gurbin dake akwai a ɓangaren ilimin jihar.

Idan zaku iya tuna wa, gwamnatin jihar ta ɗauki malamai 1,000 a farkon wannan shekarar ta hanyar bin wasu matakai masu tsauri da ya haɗa da hukumar JAMB, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Gwamnan Osun mai barin Gado, Mr Adegboyega Oyetola.
Bayan Shan Kaye a Zaɓe, Gwamna APC Zai Ɗauki Sabbin Ma'aika a Jihar Osun Hoto: leadership
Asali: Twitter

A wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Osogbo bayan taron majlisar zartaswa (SEC), Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kai, Funke Egbemode, yace matakin zai cike gurbin rashin isassun Malami a Osun.

Kara karanta wannan

Wawure N2.5bn: Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Buƙatar Kakakin Majalisar Dokoki

Egbemode, wanda ya bayyana cewa za'a fifita yankunan karkara wajen tura Malaman, ya ƙara da cewa tuni aka kafa kwamitin da zai aiki kafaɗa da kafaɗa da ma'aikatan ilimi domin ɗaukar malaman.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna mai jiran gado ya yi fatali da matakin

Kwamitin karɓan mulki da zaɓaɓɓen gwamna, Sanata Ademola Adeleke, ya kafa, wanda ya yi fatali da ɗaukar malaman, yace gwamnati mai ci ta shirya wata manaƙisa ne domin gurgunta tattalin arzikin jihar.

A cewar shugaban ƙaramin kwamitin yaɗa labarai, Mallam Olawale Rasheed, yace za'a ɗauki malaman ne da nufin ƙara wa jiha nauyi, ƙara jefa ma'aikata cikin ƙangin wahala da kuma sare guiwar ɓangaren aiki a jihar.

Ya ƙara da cewa gwamna mai jiran gado, Sanata Ademola Adeleke, ba zai yarda da abinda ya kira, "Ɓoyayyar Ajenda," da gwamna mai barin Gado ke shirin aiwatar wa mutanen jihar Osun ba.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Buhari Tace Ta Magance Mafi Munin Matsalar Tsaro a Najeriya

A wani labarin kuma Lamari Ya Kara Dagule Wa APC, Ɗaruruwan Mambobinta Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP

Yayin da rage sauran 'yan watanni a fafata zaɓen 2023, jam'iyyar APC mai mulki ta gamu da babban cikas a jihar Ondo.

Daruruwan mambobin APC a ƙaramar hukumar Ifedore sun tattara sun koma jam'iyyar PDP a wurin wani taro yau Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel