Jerin Mutanen Da Tukur Mamu Ya Yi Sanadiyyar Kubutarsu Daga Hannun 'Yan Bindiga

Jerin Mutanen Da Tukur Mamu Ya Yi Sanadiyyar Kubutarsu Daga Hannun 'Yan Bindiga

 • An kama Tukur Mamu wanda ya jagoranci sulhu don ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da yan bindiga suka yi garkuwa da su
 • An cafke Mamu, wanda ya kasance kakakin shahararren malamin nan na Musulunci, Sheikh Abubakar Gumi, tare da iyalinsa a kasar Masar
 • Wani bincike ya nuna cewa Mamu na da hannu a wajen sulhu da sakin kimanin mutane 25 da yan bindiga suka yi garkuwa da su

An kama shahararren marubucin nan mazaunin Kaduna, Tukur Mamu, wanda ya jagoranci sulhu don ceto wasu fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna a Masar.

An damke malamin musuluncin kuma kakakin shahararren malami, Sheikh Gumi, a Cairo, babban birnin kasar Masar.

Tukur Mamu
Jerin Mutanen Da Tukur Mamu Ya Yi Sanadiyyar Kubutarsu Daga Hannun 'Yan Bindiga Hoto: @pmnewsnigeria
Asali: Twitter

Daya daga cikin sulhun da ya jagoranta a baya-bayan nan ya kai ga sakin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna 5 da aka sace a ranar Talata, 2 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Mutum 43 Da Aka Sace A Masallacin A Zamfara Sun Samu Kubuta Bayan Biya Kudi, Daya Ya Mutu

Sunayen mutanen sun hada da:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

 1. Farfesa Mustapha Umar Imam
 2. Akibu Lawal
 3. Abubakar Ahmed Rufai
 4. Mukthar Shu’aibu
 5. Sidi Aminu Sharif

Tukur Mamu ya kuma jagoranci sakin wasu mutane 7 da aka yi garkuwa da su, ciki harda yaro dan watanni 18.

A ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, Mamu ya tabbatar da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Kaduna sannan ya saki hotona da sunayensu ga manema labarai, wadanda ciki harda tsohuwa yar shekaru 60 da iyalai 6.

Jerin sunayen mutanen da aka saki a ranar 10 ga watan Yuli:

 1. Aisha Hassan, tsohowar mai shekaru 60
 2. Abubakar Idris Garba
 3. Maryama Garba
 4. Ibrahim Garba
 5. Fatima Garba
 6. Imran Garba
 7. Zainab Garba mai shekara daya

A ranar Asabar, 11 ga watan Yuni, Tukur ya sanar da sakin fasinjojin jirgin kasa 11, da suka hada da mata 6 da maza 5.

Kara karanta wannan

Mun gane kuskurenmu: Wasu ‘Yan daban Siyasa Sun Ajiye Makamai, Sun Shiga APC

Ga sunayensu a kasa:

 1. Jessy John
 2. Amina Ba’aba Mohammed (Gamba)
 3. Rashida Yusuf Busari
 4. Hannah Ajewole
 5. Amina Jibril
 6. Najib Mohammed Daiharu
 7. Gaius Gambo
 8. Hassan Aliyu
 9. Peace A.
 10. Namiji (Ba a ambaci sunansa ba)
 11. Danjuma Sa’idu

Akwai zarge-zargen cewa marubunci na bangaren yan ta’addan fiye da bin bayan ra’ayin yan Najeriya.

Sau da dama ya sha karyata wadannan zargi.

Da Duminsa: Jami'an DSS Sun Cafke Tukur Mamu a Filin Jirgin Kano

A halin yanzu, mun ji cewa jami’an tsaron farin kaya na DSS, sun kama Malam Tukur Mamu a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano.

Daily Trust ta rahoto yadda ‘yan sandan kasa da kasa suka kama Mamu a birnin Cairo dake Misra kuma aka dawo da shi gida Najeriya.

Tsohon mai sasancin tsakanin ‘yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja da iyalansu, yace yana kan hanyarsa ta zuwa Saudi Arabia ne yayin da aka kama shi tare da tsare shi na sa’o’I 24 a Misra.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Ta'adda Sun kai Sabon Farmaki Abuja, Sun Tafka Mummunar Ta'asa

Asali: Legit.ng

Online view pixel