Mun gane kuskurenmu: Wasu ‘Yan daban Siyasa Sun Ajiye Makamai, Sun Shiga APC

Mun gane kuskurenmu: Wasu ‘Yan daban Siyasa Sun Ajiye Makamai, Sun Shiga APC

An samu wadanda suka yi fice wajen banga da dabar siyasa da yanzu suke nadamar danyen aikin da suka yi

Wadannan Bayin Allah sun ajiye kayan fadansu a jihar Zamfara, sun ce sun gano amfani da su aka rika yi

Baba Karami da Garba Lawal za su bada gudumuwarsu wajen cigaban Gwamnatin Bello Matawalle a Zamfara

FCT, Abuja - Wasu gungu biyu na ‘yan bangan siyasa da suka addabi mutanen jihar Zamfara, sun nemi zaman lafiya bayan sun tuba daga aikin da suke yi.

Daily Nigerian tace wadannan mutane sun yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara ta ci moriyarsu wajen yin abubuwa na kirki, a maimakon ayyukan assha.

Tubabbun ‘yan daban siyasan sun nuna nadamarsu a kan irin tada zaune-tsaye da suka rika yi da kuma hana Bayin Allah sakat saboda manufar ‘yan siyasa.

Kara karanta wannan

Yadda Ake Hada Kai da Jami’an tsaro da Jami’an Gwamnati, Ana Sace Man Najeriya

Rahoton yace wadannan mutane sun shirya domin kawowa al’ummarsu cigaba daga yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga tsagerani zuwa APC

Baba Karami da wani Garba Lawal wanda aka fi sani da Vice, sun shaidawa manema labarai cewa sun shiga APC da nufin goyon bayan gwamnatin jihar.

Baba Karami, Vice da mutanensu za su bada gudumuwarsu wajen kawo zaman lafiya a Zamfara. Jihar tana cikin inda aka fi fuskantar rashin tsaro a Najeriya.

Bello Matawalle
Bello Matawalle ya dawo APC Hoto: @LeadershipNGA
Asali: Twitter

Kakakin APC, Yusuf Idris ya yi jawabi

A wani jawabi da sakataren yada labarai na APC na reshen Zamfara, Yusuf Idris ya fitar, an ji cewa tubabbun ‘yan daban siyasar sun sallama makamansu.

Idris ya shaidawa ‘yan jarida a Abuja gungun sun jefar da sanduna da adduna, tsohon shugaban karamar hukumar Gusau, Babangida Abdullahi ya karbe su.

Abdullahi ya yi alkwarin zai damka kayan yakin tsofaffin ‘yan daban siyasar ga jami’an tsaro, hakan ya nuna da gaske sun yi ban-kwana da banga.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Karami da Lawal sun ce sun tuba ne bayan sun gano ‘yan siyasa suna amfani da su ne, a lokacin da ‘ya ‘yan manyan suke karatu domin cin ribar rayuwarsu.

Hukumar dillacin labarai tace ‘yan gungun sun sha alwashin hada-kai da Gwamnatin Bello Matawalle domin kawo zaman lafiya da cigaban Zamfara.

Kamar yadda Babangida Abdullahi ya yi masu alkawari, za a karbe su tamkar sauran ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki, muddin ba su koma gidan jiya ba.

Kulba na barna, ana cewa jaba

A game da yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, kwanaki an rahoto Sanata Ayo Akinyelure yace shugaba Muhammadu Buhari ya danne bodari ta kai.

‘Dan Majalisar Dattawan ya bayyana cewa idan ana maganar rashin gaskiya a Najeriya, ma’aikatan gwamnati ne hatsabibai, har sun fi 'yan siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel