Yan Achaba Na Kwanciya Da Matanmu, Jami’an Yan Sanda Sun Yi Zanga-zanga

Yan Achaba Na Kwanciya Da Matanmu, Jami’an Yan Sanda Sun Yi Zanga-zanga

  • Jami'an yan sanda a jihar Osun sun gudanar da zanga-zanga saboda rashin biyansu albashi tsawon watanni 18 yanzu
  • Yan sandan sun koka cewa a yanzu yan achaba da masu adaidaita suna kwanciya da matansu saboda su sun gaza daukar dawainiyansu da na yara
  • Kwamishinan yan sandan jihar ya umurce su da su dakatar da zanga-zangar nan take yayin da yace hukumomin da ya dace za su duba bukatunsu don share masu hawaye

Jihar Osun - Akalla jami’an yan sanda 480 ne suka gudanar da zanga-zanga kan zargin rashin biyansu albashin watanni 18 a Osun.

Sun yi tattaki a manyan unguwanni da mahadar Osogbo, babban birnin jihar Osun domin yin zanga-zanga, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mutum 43 Da Aka Sace A Masallacin A Zamfara Sun Samu Kubuta Bayan Biya Kudi, Daya Ya Mutu

Yan sanda
Yan Achaba Na Kwanciya Da Matanmu, Jami’an Yan Sanda Sun Yi Zanga-zanga Hoto: News Telegraph
Asali: UGC

A watan Mayun 2021 ne aka rantsar da jami’an yan sandan a hedkwatar rundunar da ke jihar Osun bayan horar da su a watan Afrilun 2021. An kwashe su aiki ne don karfafa tsarin aikin rundunar ta hanyar bayar da bayanan sirri da sauransu.

Jami’an yan sandan da suka yi zanga-zanga sanye da kayan aiki sun hadu a yankin Old-Garage inda suka yi tattaki ta Oke-Fia, Alekuwodo kafin suka mamaye gadar sama na Ola-Iya don ganin an biya masu bukatunsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun rike kwalayen sanarwa dauke da rubutu daban-daban kamar: ‘A biya mu albashinmu yanzu’, ‘yan achaba suna kwanciya da matanmu’, ‘a biya mu albashinmu na watanni 18, ‘a biya mu’, ‘albashi da alawus dinmu’ da kuma ‘watanni 18 babu ko kwabo’.

Daya daga cikin shugabannin yan sandan da ke zanga-zanga, Constable Tijani Adewale, ya ce duk da rashin biyansu albashinsu sun jajirce kan ayyukansu yana mai cewa a wannan hali da suke ciki jami’an yan sanda uku ne suka mutu a bakin aiki.

Kara karanta wannan

Ke duniya: An kama wata malamar coci dake sayen yara kanana kan kudi N50,000

Sun yi korafin cewa yan adaidaita da yan achaba sun kwace masu matayensu saboda basa iya daukar dawainiyansu da yaransu, New Telegraph ta rahoto.

Daga bisani, kwamishinan yan sandan Osun Olawale Olokode ya hadu da su a gadar Ola-Iya sannan ya umurcesu da su dakatar da zanga-zangar nan take.

Ya basu tabbacin cewa hukumomin da ya kamata za su shiga lamarinsu don magance kokensu.

Ya ce:

“Kuna kunyata rundunar da zanga-zangarku. Da kamata yayi ku karkata kokenku zuwa kwatas din da dace. Kuna damun zaman lafiyar al’umma da wannan zanga-zanga naku. Idan dai har kuna sanye da wannan inifam din, muna sanya ran ku zamo masu da’a kamar jami’in tsaro.”

Abba Kyari Ya Magantu Kan Kadarori 14 Da FG Ta Bankado A Matsayin Nasa

A wani labari na daban, dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP Abba Kyari, ya karyata batun mallakar kadarori 14 da ake zargin gwamnatin tarayya ta bankado.

Kara karanta wannan

Da Gaske Sun Yi Aure? Hotunan Ado Gwanja Da Momee Gombe Sun Haddasa Cece-kuce A Soshiyal Midiya

Kyari ya ce sabanin rahoton cewa an gano makudan kudade a asusun bankinsa, naira miliyan 2.8 ne kacal a asusunsa na UBA da kuma wani N200,000 a asusunsa na Sterling, jaridar Leadership ta rahoto.

A cewar wata sanarwa daga lauyansa, Barista Hamza Dan Tani, duk zarge-zargen da NDLEA ke yi dangane da kudade da kadarori mallakar Abba Kyari karya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel