Hotunan Ado Gwanja Da Momee Gombe Sun Haddasa Cece-kuce A Soshiyal Midiya

Hotunan Ado Gwanja Da Momee Gombe Sun Haddasa Cece-kuce A Soshiyal Midiya

  • Wasu sabbin hotunan mawaki Ado Gwanja da jarumar Kannywood, Momee Gombe sun yadu a shafukan soshiyal midiya
  • Manyan jaruman na masana'antar shirya fina-finan Hausa sun yi tsayuwar daukar hotunan tamkar sabbin ma'aurata
  • Wadannan hotuna sun haddasa cece-kuce, yayin da wasu da dama ke ganin duk shiri ne, wasu sun yi masu fatan alkhairi

Jama’a sun shiga rudani bayan bayyanar wasu hotuna na manyan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ado Gwanja da Momee Gombe a soshiyal midiya.

A cikin hotunan wadanda tuni suka yadu a shafukan sadarwa, an gano jaruman biyu cikin shiga da ta fi kama da ta sabbin ma'aurata kuma sun yi tsayuwar daukar hoto sak irin na amarya da ango.

Gwanja da Momee Gombe
Hotunan Ado Gwanja Da Momee Gombe Sun Haddasa Cece-kuce A Soshiyal Midiya Hoto: momee_gombe
Asali: Instagram

Wannan al’amari ya jefa mutane cikin shakku, yayin da wasu ke ganin shirin fim ne, wasu kuma sun yi fatan Allah yasa hakan ya zamo gaskiya.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yiwa Amaryarsa Yayyafin Kudi Bandir-bandir A Wajen Budan Kai Ya Ja Hankali

Sai dai kuma, babban abun da ya kara jefa mutane cikin duhu, shine yadda kowannensu ya je shafinsa na Instagram ya daura hotunan tare da yin wasu rubutu da ke son tabbatar da abun.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da take wallafa hotunan a shafinta mai suna momee_gombe, jarumar ta yi Hamdallah ga Ubangiji a kasan hoton.

Momee Gombe ta rubuta a takaice:

“alhamdulillah ❤️.”

A nashi bangaren, Mawaki Ado Gwanja ya wallafa hotunan dauke da rubutun:

"Lokaci @momee_gombe."

Hakazalika wasu manyan jaruman masana'antar sun sake jefa mutane cikin duhu da irin martanin da suka yi a sashin sharhi na jaruman.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

realalinuhu ya yi martani:

"Masha Allah."

officialsojaboy ya ce:

"Wannan Tafiya tayi kyau Allah Kaimu ranar ."

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

official_gadeerabadi ta ce:

"Tsaya tukunna bangane ba ."

maryaaamah_ ta ce:

"Wai dagaske ne masha Allah."

real_xubiey ya ce:

"Allah ya sanya alkhairi my rani @momee_gombe ."

sister_sameerah ta ce:

"Masha allah amrya da ango ❤️❤️."

rukkieshow ta yi martani:

"Ya sunan wakar da zaayi."

itsfarhamuhd ta ce:

"Me sunan film din."

Ga wallafar tasu a kasa:

Ba’a Kyauta Mana Mu Talakawa: Rukayya Dawayya ta Koka Kan Yadda ‘Ya’yan Masu Kudi Ke Auran Junansu A Kasar

A wani labarin, Shahararriyar jarumar Kannywood, Rukayya Umar Dawayya ta yi martani a kan yadda ake yin kwarya tabi kwarya wajen kulla auratayya a kasar nan.

Dawayya ta shawarci ‘ya’yan talakawa da ke da kyau a kan su daina yarda da soyayya tsakaninsu da yaran masu kudi domin magana ta gaskiya ba auransu za su yi ba.

A cewarta koda yaran na son su iyayensu ba za su amince a kawo masu diyar talakawa a matsayin suruka ba, don haka ta shawarce su da su tashi su nemi ilimi don gobensu.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Magantu Kan Rikicin Atiku da Wike, Ya Raɗa Wa PDP Sabon Suna

Asali: Legit.ng

Online view pixel