An Kama Malamar Coci da Yara 15, Ta Ce N50,000 Take Sayen Yaro Daya

An Kama Malamar Coci da Yara 15, Ta Ce N50,000 Take Sayen Yaro Daya

  • Wata malamar coci ta shiga hannu yayin da ake zargin tana sana'ar fataucin kananan yara a jihar Ribas
  • Rundunar 'yan sanda sun yi bayanin yadda suka kamo ta da kuma yadda aka kame wasu mutane da dama
  • Malamar ta ce takan sayi yara akan N50,000, N60,000 ko N100,000 daga hannun wani mutum da ke kawo mata su

Jihar Ribas - Wata malamar coci mai suna Maureen Wechinwu dake fataucin yara kanana ta shiga hannun jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ribas.

Rahoton jaridar Vanguard ya ce, rundunar ta kuma gurfanar da wasu mutum 20 da aka kama tsakanin watan Agusta zuwa Satumba bisa laifuka daban-daban.

Bayan samun bayanan sirri, 'yan sanda sun kama Maureen a gidanta dake Aluu ta karamar hukumar Ikwerre a jihar Ribas, tare da ceto yara kanana har 15 daga gidanta.

Kara karanta wannan

Rivers: N50,000 Na Siya Kowanne Daga Cikinsu: Rabaren Sista da Aka Kama da Yara 15

An kama wata malamar coci da ke fataucin yara
An Kama Malamar Coci da Yara 15, Ta Ce N50,000 Take Sayen Yaro Daya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Friday Eboka, ya bayyana cewa yaran da aka gano a hannun matar ‘yan shekaru bakwai zuwa tara ne, inda ya kara da cewa za’a gurfanar da ita bayan kammala cikakken bincike.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Eboka ya ce binciken farko na 'yan sanda ya nuna cewa an dauko yaran ne daga sassa daban-daban na jihohin Kudu maso Kudu a Najeriya, kuma da gaske sayensu ta yi.

A cewar kwamishinan, an dauki sama da sa’o’i 24 kafin yaran su iya yin bayani ga ‘yan sanda kan abubuwan da suka faru da su, kuma da gani an azabtar dasu ya kara da cewa ana azabtar kuma alamu sun nuna tuni an rikita tuaninsu.

Martanin malamar cocin

A bangarenta, Maureen Wechinwu, a hira da aka yi da ita, ta bayyana cewa yanzu dai ta zama abin kunya ga danginta da kuma ita kanta, inda ta dage cewa ba ta sana'ar fataucin yara.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Toshe Hanyar Kaduna, Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Matafiya Da Dama

Maureen tace:

“Gidan marayu nake gudanarwa mai dauke da ’ya’yan mahaukata. Daya daga ciki ita ce Fransisca Onyinyechi, wacce wata mahaukaciya ta haifa a kasuwar unguwar Ogbogoro."

Hakazalika, ta yi bayanin cewa, tana daya daga cikin manyan matan malamai a addinin kirista da suka samu shaida daga kasar Burtaniya.

Da take karin haske game da yadda take samo yaran ta ce:

“Wasu daga cikin yaran nan ’ya’yan mahaukata ne. Sauran kuma wani mutum ne Mr. Victor ke kawo mini su.
“Wani lokacin yakan zo da biyu. Wata mata mai suna Miss Alice ta kawo min wasu biyu."
“Wani lokaci idan Victor ya kawo min yara, yakan nemi na bashi kudi. Saboda yadda yake matsa min lamba, wani lokaci nakan ba shi N50,000, N60,000, ko N100,000."

Wasu iyayen yara sun magantu

Wasu mata biyu da suka ce sun gane yaransu daga cikin yaran da 'yan sandan suka ceto sun bayyana yadda suka gane 'ya'yansu a hedikwatar ‘yan sandan.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Glory Onyia, mahaifiyar daya daga cikin yaran ta bayyana cewa, ita dai danta bata ya yi watanni biyar biyar da suka gabata kuma gashi ta gane shi yanzu, jaridar Eagle ta tattaro.

Ta kuma ce dangi da iyalanta sun shiga jimamin batan yaron.

Wata kuwa mai suna Nkechinyere Harry ta ce diyarta Mary bata tayi a garin tallan 'bole' da ta daura mata ta fita zuwa kasuwa.

Kasar Saudiyya Ta Fara Bincike Kan Wani Bidiyon Yadda Jami’an Tsaro Suka Zane Wasu Mata

A wani labarin kuma, a ranar Laraba ne hukumomin Saudiyya suka fara bincike kan wani faifan bidiyo dake yawo da ya nuna yadda wasu jami’an tsaro ke dukan 'yan mata a gidan marayu da ke Kudu maso Yammacin kasar.

Arab News ta ruwaito cewa, gwamnan yankin Asir ya hada wani kwamiti da zai binciki dukan da aka gani yana yawo a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kwashe Matafiya 32 Dake Dawowa Daga Jana'iza a Ondo

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana halin da lamarin da ya faru na lokacin da aka dauki bidiyon da kuma dalilin dukan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel