Ruwa Yayi Awon Gaba da Sama da 'Yan Boko Haram 70 Sakamakon Luguden Sojojin Najeriya

Ruwa Yayi Awon Gaba da Sama da 'Yan Boko Haram 70 Sakamakon Luguden Sojojin Najeriya

  • Sama da mayakan ta'addancin Boko Haram 70 ne suka rasa rayukansu sakamakon neman tserewa daga luguden sojin Najeriya da suka yi
  • An gano cewa, sojojin Najeriya sun halaka 'yan ta'adda sama da 20 a kauyen Sheruri dake bama amma wasu sun tsere tare da kokarin ketare rafi
  • Babu zato balle tsammani, ruwan yayi awon gaba da su inda aka samu gawawwakin sama da 50 daga ciki yayin da ake cigaba da neman sauran a ruwan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Sama da mmutum 70 da ake zargin 'yan Boko Haram ne ruwa yayi awon gaba da su a a wani rafi bayan luguden wutan da dakarun Operation Hadin Kai suka yi a jihar Borno, majiyoyi suka tabbatar.

An tattaro cewa, sojojin Najeriya tare da hadin guiwar kungiyar tsaron farar hula, JTF, sun halaka sama da 'yan ta'addan Boko Haram 20 a kauyen Sheruri dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan Bindiga Sace Mata Masu Juna 2, da Mutum 13 a Sabon Hari

Sojojin Najeriya
Ruwa Yayi Awon Gaba da Sama da 'Yan Boko Haram 70 Sakamakon Luguden Sojojin Najeriya. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyoyi sun ce bayan farmakin Sheruri, wadanda suka tseren ruwa yayi awon gaba da su a rafin dake kusa da kauyen Dipchari dake karamar hukumar Bama a ranar Juma'a, Daily Trust ta rahoto.

"'Yan ta'addan sun tafka mummunar asara, sun rasa rayukan sama da mayaka 70 a kusa da kauyen Dipchari. A halin yanzu da muke magana, mutane da yawa daga cikin mayakan babu su babu dalilinsu," majiyar tsaro ta tabbatar.
"Da safiyar yau wurin karfe 8:30 na safe suka yi jana'izar sama da mayaka 50 a kauyen Dipchari kuma suna cigaba da neman gawawwakin sauran 'yan ta'addan.
“Sun samo gawawwaki masu yawa daga rafin amma har yanzu akwai mayakan da ba a gani ba," majiyar tace.

Har yanzu babu takardar da ta fito a hukumance daga rundunar sojin Najeriya kafin rubuta wannan rahoton, amma jama'a da yawa daga yankin sun tabbatar da wannan cigaban.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Ta Kama 'Yahoo Boys' 41 Da Dukiyoyin Da Suka Mallaka

Rundunar sojin Najeriya na samun manyan nasarori a cikin kwanakin nan a sassan kasar nan.

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Kwashe Jama'a

A wani labari na daban, 'yan bindiga a ranar Juma'a sun sace masallata masu tarin yawa daga Masallacin Juma'a na yankin Zugu dake karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan sun boye bidigoginsu a cikin kayansu kuma suka shiga masallacin yayin da liman yake dab da fara huduba, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng