Bincike Ya Fallasa Yadda Aka Saci Naira Biliyan 12 a Lokacin Tsohon Gwamnan PDP

Bincike Ya Fallasa Yadda Aka Saci Naira Biliyan 12 a Lokacin Tsohon Gwamnan PDP

  • Rafiu Ajakaye ya fitar da jawabi a game da binciken satar kudin da aka tafka a karkashin Gwamnatin PDP a Kwara
  • Anthony Iniomoh na Kamfanin SSAC and Professionals ya jagoranci binciken kudin da aka yi, ya ba gwamna rahoto
  • Daga cikin shawarwarin da aka ba Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq shi ne ya hukunta wadanda aka samu da laifi

Kwara - Kimanin Naira biliyan 11.9 ake zargin sun bace daga asusun jihar Kwara tsakanin 2011 da 2019. Premium Times ta fitar da wannan rahoto.

Binciken kudin da aka gudanar, ya bankado yadda aka cire N2bn daga asusun gwamnatin Kwara ba tare da an yi wani aiki ko biyan kwangila ba.

Sakataren yada labarai na Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq watau Rafiu Ajakaiye, ya fitar da jawabi, yana zargin gwamnatin da suka gada da laifi.

Kara karanta wannan

Muna Binciken Matawalle Kan Amfani Da Kudin Al'umma Wajen Siyan Kadarori a Abuja, EFCC

Rafiu Ajakaiye yace an fitar da kudin ne a cikin kwanaki takwas a Fubrairun 2019. Ana zargin gwamnatin PDP tayi amfani da kudin a yakin zabe.

Abdulrahman Abdulrazaq ya karbi rahoto

Kamfanin SSAC and Professionals a karkashin jagorancin Anthony Iniomoh, suka gudanar da wannan bincike, kuma suka mikawa Gwamna rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton binciken da Mai girma AbdulRahman AbdulRazaq ya karba yana cikin mujalladi biyu dauke da bayanin kudin harajin IGR, kwangiloli.

Sahara Reporters tace binciken ya hada da albashin da aka biya ma’aikata da kadarorin da aka saida da bincike a kan duk bashin da aka karba.

Gwamnan Kwara
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

A hukunta masu laifi

Ganin yadda N11, 981,268,709 suka bace daga Baitul-mali, Anthony Iniomoh ya bada shawarar a hukunta jami’an gwamnatin da ake zargi da wannan laifi.

Bugu da kari, Iniomoh da kamfaninsu sun gano yadda gwamnati ta karbi diyyar N6,023,358,444.

Kara karanta wannan

An Yanke Wutan Gidan Gwamnati da Ofisoshi Saboda Rashin Biyan Kudin Lantarki

An yi ta fitar da kudi ba tare da an san aikin da za ayi ba, a irin haka aka gano gwamnatin Kwara ta biya hukumar CAC wasu kudi na bogi a Yunin 2016.

Abdulrahman Abdulrazaq ya tsorata da abin da aka gano a binciken, yace abin da suke gudu kenan.

Rafiu Ajakaye yace an gabatar da rahoton binciken ne a gaban manyan jami’an gwamnati kamar SSG, Mamma Jubril; Ibrahim Suleiman; da Florence Oyeyemi.

AbdulGaniyu Sani; Abdulrazaq Folorunsho, Tijani Dako da Bamidele Sobiye sun samu halarta.

Abdulfatah Ahmed v EFCC

Tsakanin Mayun 2011 da 2019, Abdulfatah Ahmed ne ya rike kujerar gwamna a jihar Kwara. Tun da ya sauka daga kan mulki, hukumar EFCC take nemansa.

Sai dai Alhaji Abdulfatah Ahmed ya musanya zargin da ake yi masa, amma har yau ana bincikensa. A 2021 aka ji labari an karbe wasu gidaje da ya mallaka.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin Shagalin Dinan Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

Asali: Legit.ng

Online view pixel