An Yanke Wutan Gidan Gwamnati da Ofisoshi Saboda Rashin Biyan Kudin Lantarki

An Yanke Wutan Gidan Gwamnati da Ofisoshi Saboda Rashin Biyan Kudin Lantarki

  • Kamfanin Abuja Electricity Distribution Company sun nuna sun gaji da rashin cika alkawarin gwamnatin jihar Neja
  • A yau aka ji kamfanin ya yankewa gidan gwamna da ma’aikatun gwamnatin Neja wuta a dalilin kin biyan tsohon bashi
  • Kakakin AEDC yace sun biyo Gwamnatin jihar kudin da sun haura Naira Biliyan 1, har yau an gagara biyan wannan kudi

Niger - Kamfanin Abuja Electricity Distribution Company watau AEDC masu raba wutar lantarki a jihar Neja sun datse wutar ma’aikatun gwamnati.

Jaridar Daily Nigerian tace hakan ya biyo bayan tulin bashi da kamfanin na AEDC yake bin gidan gwamnati, ma’aikatu da hukumomin jihar ta Neja.

AEDC sun ba gwamnatin Neja wa’adi ta biya kudin, da abin ya gagara sai aka yanke masu wuta. Mako daya aka yi ana jira, amma dai abin ya faskara.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Buhari ya yi Allah wadai da kisan gillan da aka yiwa Shehin Malami a Yobe

Kamar yadda jami’in hulda da jama’a na kamfanin AEDC, Mohammed Pele ya shaidawa 'yan jarida a yau Juma’a, kudin da suke bi ya kai N1.3bn.

Mohammed Pele yace baya ga ma’aikatun gwamnatin Neja, kamfanin ya yanke wutar lantarki a gidan gwamnati da asibitin da ke fadar gwamna.

'Yan majalisa sun tsoma baki

Pele yace kwanakin baya majalisar dokokin Neja ta sa baki a maganar bashin, har aka amince gwamnati za ta biya kamfanin 80% na kudin da suke bi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lantarki
Tashar wutar lantarki Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Tun da aka yi wannan magana da ‘yan majalisar jihar, jami’in yada labarai na kamfanin yace gwamnatin Neja ba ta biya su ba, dole aka datse su.

Mai magana da yawun bakin kamfanin AEDC yace a watanni uku da suka wuce, gwamnati ta rika biyan N74m a wata a matsayin lantarkin da aka sha.

Kara karanta wannan

Atiku: Sai na mai da jami'o'in tarayya karkashin gwamnatin jiha idan na gaji Buhari a 2023

Duk da an biya kudin watannin bayan, akwai bashin N1.3b da ya taru da ba a iya ba.

Mun ji shiru har yau - AEDC

“Har yau babu wani hobbasa daga gwamnatin jiha. Mun dauki mataki bayan an kai mu bango, ba a cika alkawarin da aka yi da majalisa ta sa baki ba,”
“Ba mu da wani zabi illa mu yanke masu wuta, mu maida hankali wajen samar da wutar lantarki ga sauran abokan huldarmu a gida da wajen birni.”

- Mohammed Pele

Taurin bashin Andy Uba

Ku na da labari Sanata Andy Uba ya karbi bashin Naira Miliyan 50 daga hannun kamfanin Oranto Petroleum Ltd, amma har yau bai biya kudin ba.

Wani Alkali ya umarci a karbe dukiyar da Uba ya mallaka domin biyan bashin. Wannan ya sa aka je gidansa, aka karbe wasu daga cikin motocinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel