Muna Binciken Matawalle Kan Amfani Da Kudin Al'umma Wajen Siyan Gidaje a Abuja, EFCC

Muna Binciken Matawalle Kan Amfani Da Kudin Al'umma Wajen Siyan Gidaje a Abuja, EFCC

  • Hukumar EFCC na zargin gwamnan Zamfara da mallakan kadarorin biliyoyin naira a Abuja
  • Jami'an hukumar sun garkame daya daga cikin kadarorin wanda aka saya kudin N1.2 Billion
  • Alkalin kotu a Abuja ya yi watsi da zargin hukumar EFCC kuma yaci ta tara bisa rufe kamfanin

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC tace tana binciken gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle bisa zargin almundahana.

EFCC tace ta fara binciken gwamnan ne sakamakon bayanan da ta samu na cewa yana amfani da dukiyar al'ummar jiharsa wajen mallakan kadarorin biliyoyi a Abuja.

Hukumar tace binciken da ta fara gudanarwa ya nuna cewa gwamnan ya sayi gida mai lamba 729, Cadastral Zone C16, Idu Industrial Estate, Abuja.

Kara karanta wannan

Idan Na Taba Satar Kudin Gwamnati, Allah Ya Tsine Mana Albarka, Peter Obi

EFCC ta bayyana hakan a karar da kamfanin Fezel Nigeria Limited ya shigar da ita kotu kan kwace ofishinta karfi da yaji, rahoton TheNation.

Kamfanin Fezel yace ginin da ake zargin gwamnan da mallaka na sa ne kuma ya sayarwa kamfanin Beisha Printing Press Limited.

Amma EFCC tace karya kamfanin Fezel keyi, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ne ya sayi dukiyar ta kamfanin Beisha Printing Press Limited.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar EFCC:

"Daya daga cikin dukiyoyin da infoma ya sanar da mu shine Plot 729, Cadastral Zone C16, Idu Industrial Estate, Abuja, da aka saya N1,200,000,000.00, wanda Dr. Bello Matawalle ya biya kudi a hannu da sunan kamfaninsa (Beisha Printing Press Limited),”
EFCCn
Muna Binciken Matawalle Kan Amfani Da Kudin Al'umma Wajen Siyan Gidaje a Abuja, EFCC

EFCC ta kara da cewa ta samu labarin an fara kokarin kwashe manyan na'urorin biliyoyi daga gidan bayan gayyatar kamfanin da tayi.

Kara karanta wannan

Zulum Ya Kayar Da Wike Da Sauran Takwarorinsa, An Alantashi Matsayin Gwarzon Gwamnan Shekara

Shi yasa ta gaggauta zuwa gidan kuma aka garkame wadanda ke wajen tare da rufe shi.

EFCC tace:

"Yayinda muka samu labari, muka gaggauta damke masu kokarin kwashe kayayyaki daga gidan."
" Mun musu tambayoyi kuma muka basu beli, kuma daya daga cikinsu. Evelyn Odagundoye, da farko ta karyata yiwa Dr Bello Matawalle aiki amma daga baya da aka gudanar da bincike kan wayarta sai aka tabbatar Dr Bello Matawalle take yiwa aiki."

Amma Alkali Inyang Ekwo a hukuncin da ya yanke ranar 30 ga Agusta, 2022, ya yi watsi da zargin EFCC inda yace ba ta da hakkin rufe kamfanin.

Ya umurci EFCC kada ta sake tanka dukiyar kamfanin kuma ta biya kamfanin N1m bisa rufe musu wajen aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel