Jerin Jihohi Masu Tsadar Kalanzir da Tukunyar Gas da Jihohi Masu Arha a Najeriya

Jerin Jihohi Masu Tsadar Kalanzir da Tukunyar Gas da Jihohi Masu Arha a Najeriya

  • Tashin farashin kayan abinci a ƙasar nan ya jefa Magidanta a Najeriya cikin wahalar rayuwa
  • Abu mafi muni, bayan abinci ana bukatar karin kuɗin da za'a sayi Kalanzir ko sabunta Gas a Tukunyar Gas
  • Yayin da wasu mutane hankalinsu kwance saboda suna rayuwa a jihohi masu arhar kayan, wasu kuma jihohinsu ana tsadar Gas da Kalanzir

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa a watan Yuli, farashin Kalanzir da mutane ke amfani da shi wurin girki da kuma Gas ya sake tashi.

A cewar NBS, matsakaicin farashin Kalanzir 'yan Najeriya na biyan N789.89 duk Lita ɗaya, an samu karin kaso 3.68% daga N761.69 a watan Yuni, 2022.

Idan aka kwatanta da Farashin watan Yuli, 2022 da N397.34 farashin lita ɗaya a watan Yuli, 2021, an samu karin kaso 98.76% cikin shekara ɗaya kacal.

Kara karanta wannan

2023: Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa Zai Haɗa Karfi da Atiku, Gaskiya Ta Fito

Farashin kayayyaki a Najeriya.
Jerin Jihohi Masu Tsadar Kalanzir da Tukunyar Gas da Jihohi Masu Tsada a Najeriya Hoto: NBS
Asali: Facebook

Farashin Galan ɗaya na Kalanzir

Haka nan, hukumar NBS ta yi bayanin cewa matsakaicin Farashin Galan ɗaya na Kalanzir ɗin girki da mutane suka saya a watan Yuli, 2022 ya kasance N2,886.41, hakan ya nuna cewa an samu karin 7.98% daga N2,673.04 a watan Yuni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kididdigar Shekara-Shekara kuma ya nuna Farashin ya tashi da kashi 121.60% daga N1,302.56 a watan Yuli, 2022.

Gas ɗin girki

Farashin cika Tukunyar Gas mai ɗaukar kilogram 5KG ya tashi da kashi 4.25% a wata-wata, daga N4,218,38 a watan Yuni, 2022 zuwa N4,397.68 a watan Yuli, 2022.

A shekara zuwa shekara kuma farashin ya tashi da kashi 105.35% daga N2,141.59 da aka sayar da shi a watan Yuli, 2021.

Haka zalika idan muka leƙa Tukunyar Girki ta Gas mai cin kilo 12.5kg, farashin sabunta Gas ɗin girki a cikinta ya tashi da kashi 3.56% a kididdigar wata-wata daga N9,485.91 a Yuni, 2022 zuwa N9,824.07 a watan Yuli, 2022.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mai Magana da Yawun Rundunar 'Yan Sanda a Najeriya Ya Mutu

A alƙaluman shekara da shekara kuma farashin ya tashi da kashi 122.15% daga N4,422.32 a watan Yuli, 2022.

Jihohi Masu Arha da tsada

A farashin litar Kalanzir, Jihohi masu sauki sune:

Bayelsa - N643.06

Benuwai - N654.76

Ribas - N655.24

Nassarawa - N665.28

Delta - N685.26

A farashin Litar Kalanzir, Jihohi masu tsada sune;

Enugu- N1,003.68

Ekiti- N989.58

Osun- N949.12

Ebonyi-N946.94

Ogun-N942.59

Gas ɗin girki

Farashin cika Tunkunyar Gas mai kilo 5kg, Jihohi masu sauki sune:

Kano-N3,981.25

Yobe -N4,000.00

Bauchi -N4,071.03

Sakkwato -N4,083.33

Akwa Ibom -N4,090.91

Farashin cika Tunkunyar Gas mai kilo 5kg, Jihohi masu tsada sune:

Neja-N4,620.00

Kwara -N4,625.00

Gombe- N4,625.00

Filato- N4,650.00

Adamawa- N4,966.67

A wani labarin kuma Jerin Kananan Hukumomi 40 a Najeriya da Ba Lallai a Yi Zabe Ba a 2023

Kananan hukumomi 40 ne akalla ake yawan kai farmaki a wasu jihohin Najeriya, kuma akwai alamun ba lallai su kada kur'u a zabe mai zuwa ba saboda ta'azzarar lamarin tsaro.

Kara karanta wannan

Magajin Buhari: Sakamakon Zaɓen 2023 Zai Gigita 'Yan Najeriya, Tsohon Ɗan Majalisa

Jihohin da hakan ya shafa irinsu Kaduna da Zamfara da Imo da Neja da kuma Sokoto ne, kasancewar 'yan ta'adda sun tasa yankunan a gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel