2023: Peter Obi Zai Koma Bayan Atiku, Daraktan Kamfe Ya Bayyana Gaskiya

2023: Peter Obi Zai Koma Bayan Atiku, Daraktan Kamfe Ya Bayyana Gaskiya

  • Tsohon gwamnan jihar Anambra mai neman gaje Buhari ya musanta rahoton janye wa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP
  • Peter Obi, mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar Labour Party ya ce 'yan Najeriya na tare da shi kuma shi ne a gaba a 2023
  • Daraktan yakin neman zaɓen Obi-Datti Ahmed, ya ce rahoton karya ce kuma matasa na tare da Obi

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party (LP), Peter Obi, ya musanta raɗe-raɗin cewa ya shirya mara wa Atiku Abubakar na PDP baya domin lashe zaɓen 2023.

Darakta Janar Na kanfen Obi- Ɗatti Ahmed, Doyin Okupe, shi ne ya yi fatali da jita-jitar a wata sanarwa da aka aike wa jaridar Leadership ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mai Magana da Yawun Rundunar 'Yan Sanda a Najeriya Ya Mutu

Peter Obi.
2023: Peter Obi Zai Koma Bayan Atiku, Daraktan Kamfe Ya Bayyana Gaskiya Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Okupe ya bayyana Obi a matsayin mafi karɓuwa a dukkan sassan Najeriya masu kuri'u mafi rinjaye kuma mutum ɗaya tilo mai kwarewar ceto Najeriya daga ƙaƙanikayin da take ciki.

Saboda haka, Okupe, ya bayyana cewa ba yadda za'ai ɗan takara karkashin inuwar LP ya tsaya yana tantamar ɗaukar makamancin wannan matakina janye wa ko goyon bayan wani ɗan takara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okupe ya ce:

"Ina mai watsi da karerayin dake yawo cewa Peter Obi ya cimma matsaya da Atiku Abubakar, mai neman kujerar shugaban ƙasa a inuwar PDP game da babban zaben 2023."
"Da ikon Allah, karbuwa mata iya da goyon bayan 'yan Najeriya na gida da na waje kuma musamman matasa, Obi zai sha gaban dukkan 'yan takarar shugaban ƙasa."
"Saboda haka ba zamu tattauna da wani ɗan takarsa dake hanyar faɗuwa zaɓe ko jam'iyyarsa. Muna kira ga Al'umma su yi fatali da farfagandar da ake yaɗa wa, wacce muna da tabbacin ba daga Atiku ta hito ba."

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa da Wani Minista Sun Yi Yunkurin Mana Karfa-Karfa a Zaben Jihata, Gwamna Ya Tona Asiri

Jagaba ne zai lashe zaɓen 2023 - Malami

A wani labarin kuma Wani Babban Malami Ya Bayyana Sunan Wanda Zai Gaji Buhari a 2023, yace sako ne daga Allah

Wani Malami ya bayyana maganar Manzanci cewa ɗan takarar APC, Bola Tinubu, ne zai gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023.

A shekarar 2019, Malamin Cocin ya yi hasashen shugaba Buhari zai lashe zaɓe karo na biyu, haka Sanata Omo-Agege.

Asali: Legit.ng

Online view pixel