Abincinki Ko Dadi Babu: Karamar Yarinya Ta Yiwa Mahaifiyarta Ba’a A Bidiyo Mai Ban Dariya, Uwar Ta Yi Martani

Abincinki Ko Dadi Babu: Karamar Yarinya Ta Yiwa Mahaifiyarta Ba’a A Bidiyo Mai Ban Dariya, Uwar Ta Yi Martani

  • Wata kyakkyawar mata ta cika da mamaki bayan karamar diyarta ta fada mata cewa bata girka abinci mai dadi a gida
  • A wani bidiyo mai ban dariya, mahaifiyar yarinyar ta kwabi diyar tata kan kasancewarta mai surutu da yin fitsarin kwance kullun
  • Da take martani sai wannan karamar yarinyar ta rama abun da mahaifiyarta tayi mata ta hanyar cewa bata girka abinci mai dadi kuma tana munshari idan tana bacci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani bidiyo mai ban dariya wanda ya yadu a soshiyal midiya ya nuno yadda wata uwa da diyarta suke yiwa junansu ba’a.

Sun shiga wani gasa yar yayi da ke yawo TikTok wanda ya bukaci mutane biyu ko fiye da haka su yi magana a kan junansu.

'Ya da uwa
Abincinki Ko Dadi: Karamar Yarinya Ta Yiwa Mahaifiyarta Ba’a A Bidiyo Mai Ban Dariya, Uwar Ta Yi Martani Hoto: @kkpalmer29
Asali: UGC

Da take martani game da diyar tata, sai uwar ta bayyana cewa yarinyar na da surutu kuma tana fitsarin kwance.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Magidanci Yayi Sadaukarwa, Ya Tura Matarsa Turai, Ya Zauna a Gida Uganda

Kalamanta:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Zan mika wayar ga mutum mai surutu amma bata san yadda za ta yi fenti kan layi ba. Tana fitsarin kwance.”

Da take martani kan haka, karamar yarinyar ta amsa da:

“Zan mika wayar ga mutum wanda bai iya girka abinci mai dadi ba kuma wanda ke bacci da munshari rghhhhhh.”

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani kan wannan bidiyo mai ban dariya

@colour_me_sweet ta ce:

“Wani abu game da yara…basa karye.”

@simphiwe_bunny ta yi martani:

“Bari na fada maki fita zan yi bayan wajen girkin.”

@amahkobu ta rubuta:

"Hahaha kawai kina ta tonowa. Wannan bangaren girkin imma wasa ne ko akasin haka, zai tsaya maki a rai.”

@onyinyejohnobute ta yi martani:

“Na matsu da son sanin abun da ya faru bayan wannan bidiyon.”

@lexymajoang ta ce:

Kara karanta wannan

Surukar Arziki: Bidiyon Sha Tara Ta Arziki Da Uwar Miji Ta Yiwa Matar Danta Ya Ja Hankali

“Wannan wasan na da matukar hatsari. Ba za mu buga sa ba a gidana. Abubuwan da zan ji.”

Bidiyo: Matashi Ya Bayyana Yadda Rayuwarsa Ta Sauya Bayan Ya Dauki Yarinyar Da Mai Tabin Hankali Ta Jefar

A wani labarin, wani matashin dan Najeriya mai suna Ben-Kingsley Nwashara ya shahara bayan ya dauki wata karamar yarinya yar shekaru biyu da aka jefar a bakin hanya zuwa gidansa.

Ya bayyana cewa mahaifiyar yarinyar wacce ke da lalurar tabin hankali ce ta watsar da ita. Bayan ya dauke ta, Ben ya ce ya kaita ofishin yan sanda sannan daga bisani ya kai ta gida.

A cewar Ben, rayuwarsa ta kara kyau tun bayan da yarinyar ta shigo rayuwar tasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel