Bidiyo: Matashi Ya Bayyana Yadda Rayuwarsa Ta Sauya Bayan Ya Dauki Yarinyar Da Mai Tabin Hankali Ta Jefar

Bidiyo: Matashi Ya Bayyana Yadda Rayuwarsa Ta Sauya Bayan Ya Dauki Yarinyar Da Mai Tabin Hankali Ta Jefar

  • Wani matashin dan Najeriya wanda ya tsinci yarinya a bakin hanya ya bayyana halin da yake ciki watanni bayan ya dauke ta
  • An gano kyakkyawar yarinyar ne kwance a kasa bayan mahaifiyarta wacce ke fama da tabin hankali ta yasar da ita
  • Bayan ya hango yarinyar, sai matashin ya dauke ta, kuma a cewarsa tun bayan nan rayuwarsa ta sauya

Najeriya - Wani matashin dan Najeriya mai suna Ben-Kingsley Nwashara ya shahara bayan ya dauki wata karamar yarinya yar shekaru biyu da aka jefar a bakin hanya zuwa gidansa.

Ya bayyana cewa mahaifiyar yarinyar wacce ke da lalurar tabin hankali ce ta watsar da ita. Bayan ya dauke ta, Ben ya ce ya kaita ofishin yan sanda sannan daga bisani ya kai ta gida.

Matashi da yarinya
Bidiyo: Matashi Ya Bayyana Yadda Rayuwarsa Ta Sauya Bayan Ya Dauki Yarinyar Da Mai Tabin Hankali Ta Jefar Hoto: BBC Pidgin
Asali: Instagram

Ben ya kira yarinyar mai shekaru 2 a matsayin alkhairi gare shi

A cewar Ben, rayuwarsa ta kara kyau tun bayan da yarinyar ta shigo rayuwarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce a yanzu yana tunani mai kyau fiye da yadda yake yi a baya kuma ya kara samun nasara. Ya jadadda cewa bait aba danasanin daukar yarinyar daga titi ba.

Matashin ya kuma bayyana cewa zai tabbatar da ganin yarinyar ta je makaranta har sai ta samu digirin digir-gir.

Jama’a sun yaba masa

Christiana Ngozi ta ce:

“Allah ya albarkace ka sannan ya bude maka hanyoyin da babu mai iya rufewa muddin rayuwarka Amin.”

Maryam Precious ta ce:

“Rayuwa na da matukar kyau. Ba wai rayuwarka kadai ka canja ba ill aka canja rayuwar wannan yar karamar yarinyar har abada. Godiya ga Allah madaukakin sarki ga kyakkyawar zuciyarka, kuma Allah ya albarkaceka da kyakkyawar diyarka da dukkan abun da kake yiwa kanka fata, amin.”

Chinenye Ikenna ta yi martani:

“Kan wannan abu da kayi, Allah zai ci gaba da yima albarka da aikin hannunka. Aljihunka ba zai taba bushewa ba muddin rayuwarka.”

Kalli bidiyon a kasa:

Soyayya Na Bi: Matashiyar Da Ta Baro Birni Ta Koma Rayuwa A Unguwar Talakawa Ta Magantu A Bidiyo

A wani labarin, Oluwafunmilayo Fatai, wata matashiya yar Najeriya ta jefa yan uwa da abokanta cikin halin mamaki lokacin da ta yanke shawarar komawa unguwar matalauta a Lagas don fara rayuwa da mutumin da ta aura a chan.

Tsawon shekaru shida, malamar makarantar bata taba da na sanin barin birni don fara rayuwa da burin ranta ba.

A wata hira ta musamman tare da Legit TV, matar wacce ke da yara uku a yanzu ta bayyana cewa ta auri maigidan nata a 2016.

Asali: Legit.ng

Online view pixel