Bidiyo: Yadda Magidanci Yayi Sadaukarwa, Ya Tura Matarsa Turai, Ya Zauna a Gida Uganda

Bidiyo: Yadda Magidanci Yayi Sadaukarwa, Ya Tura Matarsa Turai, Ya Zauna a Gida Uganda

  • Wani jajirtaccen miji ya tura matarsa Turai yayin da shi ya tsaya a kasarsu tunda basu da kudin tafiya su dukka biyun
  • Matarsa wacce ta cika da farin ciki ta yada wani bidiyo tana mai nuna farin cikin samun jajirtaccen mutum a matsayin miji
  • Masu amfani da TikTok wadanda suka ga bidiyon sun cika da mamaki sannan sun jinjinawa mijin matar

Uganda - Wata mutuniyar kasar Uganda ta kwararo ruwan yabo kan mijinta bayan ya turata kasar waje sannan shi ya zauna a gida Uganda.

A cewar matar, ta dade tana mafarkin zuwa Turai, sai gashi mijin nata ya sa mafarkinta ya zama gaskiya.

Matar aure
Bidiyo: Yadda Magidanci Yayi Sadaukarwa, Ya Tura Matarsa Turai, Ya Zauna a Gida Uganda Hoto: TikTok/@mubeezi.
Asali: UGC

A wani dan gajeren bidiyo da ta wallafa a TikTok, matashiyar matar tace basu da kudin su dukkansu biyu za su yi tafiyar a tare, don haka mijin nata ya sadaukar mata.

Kara karanta wannan

Surukar Arziki: Bidiyon Sha Tara Ta Arziki Da Uwar Miji Ta Yiwa Matar Danta Ya Ja Hankali

Ta rubuta a jikin bidiyon:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mijina bai da isasshen kudin da mu duka biyu za mu je Turai. Don haka ya turani ni kadai yayin da shi ya tsaya a Uganda, na dade ina mafarkin zuwa Turai. Ina kokarin ganin na ji dadi ba tare da shi amma tuni na fara kewarsa.”

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@yondis2015 ta ce:

"Ina fatan za ki ya aiki tukuru sannan shima ki kawo sa."

Tina & Oskar ta yi martani:

"Awww, wannan ya sani hawaye, yanzu wannan ita ce soyayya ta gaskiya."

@cidygatwiri ta yi:

"Ke mace ce mai karfin zuciya...Bana iya barci ba tare da mijina ba...Ban san me ke damuna ba."

@ProudMufumbira ta yi martani:

"Ki ajiye shi a zuciya...kada ki manta da shi. Irinsa ne kake ajiyewa a matsayin amini."

Kara karanta wannan

Aljannar Duniya: Bidiyon Katafaren Jirgin Sama Mai Dauke Da Dakunan Barci 2 Ya Yadu A Soshiyal Midiya

Surukar Arziki: Bidiyon Sha Tara Ta Arziki Da Uwar Miji Ta Yiwa Matar Danta Ya Ja Hankali

A wani labarin, wata yar Najeriya mai amfani da sunan @oliviawhitehairs ta yi fice a soshiyal midiya bayan ta bayyana cewa ta yi dacen uwar miji yayin da ta wallafa wani bidiyon sha tara ta arziki da ta kawo mata.

A wani bidiyo da ta wallafa a TikTok, matar ta cika da murna cewa uwar mijinta ta zo daga kauye sannan ta kawo kayan abinci masu yawan gaske.

Da take daukar bidiyon kayan abincin da ta kawo, matar ta nuna doya da yawa, kullin bushashhen kifi, rabin buhun shinkafa, sinkin ayaban suya, katon buhun garin rogo da sauran kayan amfanin gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel