Surukar Arziki: Bidiyon Sha Tara Ta Arziki Da Uwar Miji Ta Yiwa Matar Danta Ya Ja Hankali

Surukar Arziki: Bidiyon Sha Tara Ta Arziki Da Uwar Miji Ta Yiwa Matar Danta Ya Ja Hankali

  • Wani dan gajeren bidiyo ya nuno lokacin da wata matar aure ke murna bayan ta ga tulin kayan abinci da uwar mijinta ta kawo mata
  • A cikin kayan abincin akwai kullin bushashhen kifi da katon buhun garin rogo
  • Yan Najeriya da dama da suka yi martani kan bidiyon matar sun bayyana cewa ta yi dace da uwar miji kuma dole ta kula da ita

Najeriya - Wata yar Najeriya mai amfani da sunan @oliviawhitehairs ta yi fice a soshiyal midiya bayan ta bayyana cewa ta yi dacen uwar miji yayin da ta wallafa wani bidiyon sha tara ta arziki da ta kawo mata.

A wani bidiyo da ta wallafa a TikTok, matar ta cika da murna cewa uwar mijinta ta zo daga kauye sannan ta kawo kayan abinci masu yawan gaske.

Matar aure da kayan abinci
Surukar Arziki: Bidiyon Sha Tara Ta Arziki Da Uwar Miji Ta Yiwa Matar Danta Ya Ja Hankali Hoto: TikTok/@oliviawhitehairs
Asali: UGC

Da take daukar bidiyon kayan abincin da ta kawo, matar ta nuna doya da yawa, kullin bushashhen kifi, rabin buhun shinkafa, sinkin ayaban suya, katon buhun garin rogo da sauran kayan amfanin gida.

Duba ga kayayyakin, mutum zai yi tunanin matar za ta bude shagon siyar da kayan abinci ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Mo ta ce:

“Haka uwar mijina take nima.”

userpeecharles ta ce:

“Kin yi sa’a sosai.”

uju940 ta ce:

“Matar kirki ce.”

sexyib ta ce:

“Wannan uwar mijin ta yi.”

Kyawawan Hotunan Daurin Auren Wasu Yan Najeriya A Dubai Ya Yadu, Sun Yi Shaglin Bikinsu A Saukake

A wani labarin, wani dan Najeriya mai suna Duru C.E. ya angwance da kyakkyawar budurwarsa a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sai dai wasu mutane sun lura cewa babu wasu baki da suka halarci daurin auren yayin da aka gano mutumin tare da matarsa kadai a wajen karbar takardar shaidar zama ma’aurata.

Sai dai kuma, Duru ya ce akwai gagarumin shagalin bikin da zai zo a nan gaba bayan masu amfani da Twitter sun fara sharhi game da yadda ya yi bikinsa cikin sauki baki a lekun daga shi dai amaryarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel