Ya Guje Mu Saboda Baya Son Tagwaye: Bidiyon Sauyawar Wata Mata Da Yan Biyunta Ya Ba Da Mamaki

Ya Guje Mu Saboda Baya Son Tagwaye: Bidiyon Sauyawar Wata Mata Da Yan Biyunta Ya Ba Da Mamaki

  • Bidiyon wata kyakkyawar mata da tagwayen yan matanta ya yadu a shafukan soshiyal midiya bayan ta saki hotunansu na da da yanzu
  • Rubutun da bidiyon ke dauke da shi ya nuna cewa mahaifin yaran ya guje su saboda baya kaunar tagwaye
  • Sai dai kuma sun ce a yanzu da rayuwarsu ta sauya yana neman su dawo gare shi amma sun yi masa nisa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan sun yi arba da bidiyon wata mata da kyawawan yan matanta biyu a shafukan soshiyal midiya.

Bidiyon na kunshe da hotunan matar da yan tagwayenta lokacin suna kanana da kuma bayan sun girma sun zama cikakkun yan mata.

Uwa da 'ya'yanta
Ya Guje Mu Saboda Baya Son Tagwaye: Hotunan Sauyawar Wata Mata Da Yan Biyunta Ya Ba Da Mamaki Hoto: twinz_love
Asali: Instagram

A cikin bidiyon wanda shafin yaran mai suna twinz_love ya wallafa a Instagram, sun rubuta cewa mahaifinsu ya guje su saboda baya son tagwaye wanda hakan ke nufin mahaifiyarsu ita daya tayi fadi tashi a kansu har suka zama mutane.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Magidanci Yayi Sadaukarwa, Ya Tura Matarsa Turai, Ya Zauna a Gida Uganda

Har ila yau an hasko inda suka zama manyan mata wanda kallon su kadai zai nuna maka suna cikin jin dadin rayuwa, sannan a kasan hoton an rubuta cewa a yanzu yana so su dawo gare shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta rubuta:

“Ya barmu saboda baya son tagwaye. Yanzu yana so mu dawo gare shi lol.”

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Tuni jama’a suka cike sashin sharhi don bayyana ra’ayoyinsu yayin da suka jinjinawa matar a kan wannan kokari da tayi da yaran nata. Ga wasu daga cikin martanin a kasa:

iamtrinityguy ya yi martani:

"Alhamdulila robilhalamin ❤️❤️❤️"

monalisa.stephen ta ce:

"Kada ku karbe shi fa ."

froshteefah ta ce:

"Allah abun godiya❤️."

doubledstwins ya ce:

"Allah ne mafi girma ."

Ya Rabu Dani Saboda Muni: Hotunan Sauyawar Wata Budurwa Shekaru Bayan Saurayi Ya Guje Ta Ya Ba Da Mamaki

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Haifi Yan 4 Bayan Shekaru 7 Tana Jiran Tsammani, Bidiyon Ya Dauki Hankali

A wani labarin, mun ji cewa wani saurayi na nan yana danasani a yanzu. Hakan ya samo asali ne bayan bidiyon sauyawar wata budurwa da ya watsar saboda “muni” sun yadu a soshiyal midiya kuma ta birge mutane da dama.

Wata mai amfani da dandalin TikTok Dorothy Cornelius @dorothycorneliusa ta je shafinta don yada hotunanta, wanda ke nuna yadda kamanninta suke a shekarun baya da kuma yadda take a yanzu.

Ta yi rubutu kamar haka a jikin bidiyon: “Ya yi watsi da ni saboda ina da muni, mai kama da namiji, da kuma hayaniya.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel