Ya Rabu Dani Saboda Muni: Hotunan Sauyawar Wata Budurwa Shekaru Bayan Saurayi Ya Guje Ta Ya Ba Da Mamaki

Ya Rabu Dani Saboda Muni: Hotunan Sauyawar Wata Budurwa Shekaru Bayan Saurayi Ya Guje Ta Ya Ba Da Mamaki

  • Bidiyon wata kyakkyawar budurwa ya yadu a shafukan soshiyal midiya bayan ta saki tsoffi da sabbin hotunanta
  • Rubutun da bidiyon ke dauke da shi ya nuna cewa wani saurayi ya taba gudun ta saboda kamanninta
  • Bidiyon wanda ya samu mutane sama da 2,000 da suka kalle shi, ya kuma nuno yadda budurwar ta sauya a yanzu ta kara kyau fiye da lokutan baya

Ko shakka babu wani saurayi na nan yana danasani a yanzu. Hakan ya samo asali ne bayan bidiyon sauyawar wata budurwa da ya watsar saboda “muni” sun yadu a soshiyal midiya kuma ta birge mutane da dama.

Wata mai amfani da dandalin TikTok Dorothy Cornelius @dorothycorneliusa ta je shafinta don yada hotunanta, wanda ke nuna yadda kamanninta suke a shekarun baya da kuma yadda take a yanzu.

Kara karanta wannan

Matar Da Ta Haifi Yan 4 Ta Wallafa Kyawawan Hotunan Lokacin Da Take Goyon Ciki

Budurwa
Ya Rabu Dani Saboda Muni: Hotunan Sauyawar Wata Budurwa Shekaru Bayan Saurayi Ya Guje Ta Ya Ba Da Mamaki Hoto: @dorothycorneliusa/TikTok
Asali: UGC

Ya yi watsi da ni

Ta yi rubutu kamar haka a jikin bidiyon:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ya yi watsi da ni saboda ina da muni, mai kama da namiji, da kuma hayaniya.”

Da alama Dorothy ta kasance mara adana a lokacin da take matashiyar budurwa, amma a yanzu ta sauya ta zama hadaddiyar budurwa wacce ko shakka babu duk inda ta shiga za a kalle ta a sake kallo. Koda yake ta yarda cewa har yanzu tana da hayaniya.

Sauyawatar ya burge mabiya shafinta da dama inda suka tofa albarkacin bakunansu.

Kalli bidiyon a kasa:

Ga wasu daga cikin martanin mutane a kasa:

Baby Rihanna ta rubuta:

“Wow, ina ta danna “like” a bidiyoyinki kuma ban san makaranta ta kika gama ba.”

Nana Kwame ta ce:

“Wannan shine mafi kyawu da na gani zuwa yanzu.”

Kara karanta wannan

Na Hadu Da Shi Bai Da Ko Waya: Budurwa Ta Kasance Da Saurayinta Har Ya Siya Motar Benz

Dolly D ta yi martani:

“Kina da kyau️.”

namina263 ta rubuta:

“Tana da kyau tun a baya eiii...”

user9442087237270 ya yi martani:

“Wannan sauyin ya zo da karfi.”

Ku Kama Ni: Hotunan Kyawawan Yan Gida Daya Da Ke Aikin Yan Sanda Ya Gigita Samari

A wani labarin, wasu kyawawan yan mata yan gida daya wadanda ke aiki a matsayin jami’an yan sandan Najeriya sun yi fice bayan hadaddun hotunansu sun yadu a soshiyal midiya.

Karamar cikinsu ta je shafin TikTok don wallafa hotunan da suka dauka tare da yayar tata kala-kala, inda ta bayyana cewa tana matukar kewarta.

Hoton farko da ta daura ya nuno wasu kyawawan yan mata tsaye a gaban ofishin yan sanda cikin shigar yan sanda ta bakin kaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel