Wasu Sojojin Najeriya Sun Mutu A Harin Kwanton Bauna A Zamfara

Wasu Sojojin Najeriya Sun Mutu A Harin Kwanton Bauna A Zamfara

  • Harin kwanton bauna na wasu yan bindiga a Zamfara ya kashe dakarun sojojin Najeriya guda uku a karamar hukumar Bungudu
  • Wata majiya daga garin Bungudu ta ce sojojin suna kan hanyarsu ne na zuwa amsa kiran neman dauki a wasu garuruwa sai yan bindigan suka afka musu
  • Amma, sojojin ba su yi kasa a gwiwa ba domin sun mayar da wuta sun kuma kashe wasu cikin yan bindigan da suka kai musu harin

Zamfara - Yan bindiga a ranar Laraba sun kashe sojoji guda uku a wani harin kwanton bauna da suka kai musu a karamar hukumar Bungudu, Daily Trust ta rahoto.

Mazauna garin sun ce maharan sun tsare motoccin sojojin ne a hanyarsu na zuwa kai dauki ga mutanen Fanda-Haki, Yar Katsina da Karrakkai da bata gari suka kaiwa hari.

Kara karanta wannan

Hamisu Wadume: An sake Sojojin Da Suka Kashe Yan Sanda, Har An Karawa Kyaftin Balarabe Girma

Taswirar Jihar Zamfara.
Sojoji 3 Sun Mutu A Wani Harin Kwanton Bauna A Jihar Zamfara. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani mazauna garin da abin ya faru ya magantu

Wani mazaunin garin mai suna Hussaini Ali ya ce:

"An sanar da sojojin game da harin da aka kaiwa garuruwan sai suka kama hanya zuwa tafi kai dauki amma kwatsam sai bata gari suka tare su suka bude musu wuta."

Amma, mazauna garin sun ce sojojin sun mayar da martani sun kashe da yawa cikin maharan ya kara da cewa sojojin sun tilastawa maharan tserewa.

Ali ya kara da cewa:

"Kasuwar ranar Alhamis babban kasuwa ne a Bingi amma yan kasuwa da masu sayayya sun takaita zirga-zirgansu saboda tsoron mahara. Saboda ta yiwu yan bindigan za su fusata saboda mutanensu da aka kashe."

Ba a samu ji ta bakin kakakin sojoji a jihar ba, Kyaftin Ibrahim Yahaya, domin ba a same shi a waya ba a lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Ayarin Sojoji Kwantan Bauna, An Yi Kazamar Musayar Wuta, Da Yawa Sun Mutu

Harin Kwanton Bauna: Yan Bindiga Sun Afka Wa Tawagar Yan Sanda Sun Kashe Jami'i Daya

A wani rahoton, wasu yan bindiga da ake zargin yan kungiyan asiri ne, a safiyar ranar Asabar sun kai wa motar sintiri na yan sanda harin kwanton bauna a Banga Camp kan gadar Swali a karamar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa, inda suka kashe jami'i daya.

Wata majiya daga garin Swali ta shaida wa Daily Trust cewa bata garin sun mamayi jami'an tsaron ne suka yi musayar wuta na tsawon wani lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel