Yan Bindiga Sun Mamayi Sojoji, Sun Buɗe Musu Wuta a Jihar Zamfara

Yan Bindiga Sun Mamayi Sojoji, Sun Buɗe Musu Wuta a Jihar Zamfara

  • Yan bindiga sun yi wa ayarin sojoji kwantan ɓauna, an yi kazamar musayar wuta a yankin ƙaramar hukumar Bungudu, jihar Zamfara
  • Mazauna yankin da abun ya faru sun ce dakarun sun maida martani kuma sun kashe dandazon yan bindigan nan take
  • Mataimakin gwamnan Zamfara ya ce manyan shugabannin yan bindiga har da Bello Turji sun rungumi zaman lafiya

Zamfara - 'Yan bindiga sun yi wa Dakarun sojoji kwantan ɓauna a ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara ranar Laraba, sun kashe mutum uku, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna yankin sun bayyana cewa yan ta'addan sun mamayi Motar Sojojin ne yayin da suke kan hanyar kai ɗauki ƙauyukan Fanda-Haki, Yar Katsina da Karrakkai, inda suka samu bayanan sirri na kai hari.

Sojojin Najeriya.
Yan Bindiga Sun Mamayi Sojoji, Sun Buɗe Musu Wuta a Jihar Zamfara Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wani ɗan yankin mai suna, Hussaini Ali Ya ce:

"Sojojin sun samu bayanin shirin kai hari ƙauyukan, suka yanke zuwa can don dakile harin amma ayarin motocin su na cikin tafiya ba zato sai ƴan ta'adda suka buɗe musu wuta."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai a cewar mutane, Sojojin sun maida martani kuma sun kashe yan bindiga da yawan gaske, luguden wutan sojojin ya tilasta wa yan ta da ƙayar bayan tsere wa.

"Alhamis ranar cin kasuwa ce a garin Bingi amma yan kasuwa da masu saye ba su fita ba ranar saboda tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo."

"Mutane sun yanke haka ne saboda fushin da ka iya yuwuwa an ƙunsa wa ƴan ta'addan domin dakaru sun kashe mayaƙan su tururu," inji Ali.

Mai magana da yawun rundunar sojojin da ke aiki a Zamfara, Kaftin Ibrahim Yahaya, ba'a same shi ba yayin da aka tuntuɓe shi domin ya yi tsokaci ta wayar salula.

A wani labarin kuma 'Yan Sanda Sun Kai Samame Sansanin Yan Bindiga a Katsina, Sun Sheke Dan Ta'adda

Dakarun yan sanda sun kai samame sansanin yan bindiga a kauyen Anguwan Mai Zuma, ƙaramar hukumar Ɗanja a Katsina.

Rundunar yan sanda ta ce yayin samamen, Jami'ai sun sheke ɗan ta'adda ɗaya, sun kwato kayan aikin su da yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel