Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 18, Sun Kwato Makamai a jihar Benuwai

Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 18, Sun Kwato Makamai a jihar Benuwai

  • Yan bindigan da ke garkuwa da mutane su 18 sun shiga hannun dakarun yan sanda a jihar Benuwai da ke arewacin Najeriya
  • Bayanai sun nuna cewa da taimakon mutanen gari, yan sanda suka kama waɗan da ake zargin a Ikpayongo, ƙaramar hukumar Gwer
  • Hukumar yan sanda reshen jihar Benuwai ta tabbatar da cigaban, inda ta ce a yanzu tana kan bincike

Benue - Dakarun hukumar yan sanda reshen jihar Benuwai sun yi ram da ƴan bindiga masu garkuwa da mutane su 18 kuma sun kwato wasu makamai a hannun su.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan, Anene Sewuese Catherine, ita ce ta tabbatar da wannan nasarar ranar Litinin, kamar yadda rahoton Channels tv ya tabbatar.

Yan sanda sun kama masu garkuwa.
Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 18, Sun Kwato Makamai a jihar Benuwai Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ta ce masu garkuwan da ake zargin sun yi kokarin kauce wa shingen binciken ababen hawa na yan sanda amma wasu bayanan sirri ya sa aka tura jami'ai hanyar da suka bi.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Yace Zai Iya Tuka Mota daga Abuja Zuwa Kaduna Ba Jami'an Tsaron Lafiyarsa

A cewar kakakin yan sanda, yayin binciken waɗan da ake zargi jami'ai sun samu bindigar AK47 da Bindiga mai carbi ɗauke da Harsasai 30 a tattare da su, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A sanarwan, mai magana da yawun yan sandan ta ce:

"Mun samu bayanan sirri ranar 21 ga watan Agusta, 2022 da karfe 7:30 na safe cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne na kokarin kauce wa shingen bincike da ke Titin Utonkon, ƙaramar hukumar Ado."
"Nan da nan aka tura dakarun yan sanda da haɗin kan al'ummar yankin suka yi nasarar haɗuwa da su kuma suka cafke mutane 18 da ake zargi duk maza a Ikpayongo, karamar hukumar Gwer."
"Abubauwan da yan sanda suka gano tattare da mutanen sun haɗa da AK47 guda ɗaya, da Bindigar Magazine maƙare da harsasai 30, yanzu haka muna kan gudanar da bincike."

Kara karanta wannan

Mummunar Ambaliya Ta Cinye Rayukan Mutum 10, Ta Raba Dubbanin Mutane da Muhallan Su

A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Kai Samame Sansanin Yan Bindiga a Katsina, Sun Sheke Dan Ta'aadda

Dakarun yan sanda sun kai samame sansanin yan bindiga a kauyen Anguwan Mai Zuma, ƙaramar hukumar Ɗanja a Katsina.

Rundunar yan sanda ta ce yayin samamen, Jami'ai sun sheke ɗan ta'adda ɗaya, sun kwato kayan aikin su da yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel