Dakarun Soji Sun Kai Samame Kasuwar Yan Ta'adda, Sun Kashe Wasu A Jihar Borno

Dakarun Soji Sun Kai Samame Kasuwar Yan Ta'adda, Sun Kashe Wasu A Jihar Borno

  • Sojojin Najeriya na runduna ta 21 sun ragargaji wata haramtacciyar kasuwar ƴan ta'addan Boko Haram da ke Bama a jihar Borno
  • Masani kuma mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama, ya ce sojin sun kashe yan ta'adda Shida sun kama gomman su a samamen
  • Rahoto ya nuna cewa ana kasuwancin Masara, Wake, Gishiri da sauran su da ƴan ta'addan a matsayin musaya da ƙarfe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Rundunar soji ta 21 da ke sansani a Bama ta hallaka mayaƙan kungiyar yan ta'addanci Boko Haram yayin da suka kai samame wata kasuwa da yan ta'adda suka kafa ba bisa ƙa'ida ba a ƙaramar hukumar Bama, jihar Borno.

Daily Trust ta rahoto cewa Sojojin tare da haɗin guiwar yan Sa'kai na Civilian Joint Task Force (CJTF) sun kai samame kasuwar ne da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ba Zamu Yarda Ba, A Gaggauta Hukunta Sojojin Da Suka Kashe Sheikh Aisami, IZALA Ta Yi Martani

Sojojin Najeriya.
Dakarun Soji Sun Kai Samame Kasuwar Yan Ta'adda, Sun Kashe Wasu A Jihar Borno Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa jami'an tsaron cikin shiri suka mamaye Kasuwar wacce ake kira 'Kasuwar Daula' dake ƙauyen Bararam, a yankin Bama, suka buɗe wa tsagerun wuta.

A cewar Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, ana tsaka da gudanar da harkokin Kasuwanci lokacin da Sojoji suka danno suka tsarwatsa kasuwar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce yayin da yan tada ƙayar bayan suka ga shigowar sojojin, nan take suka buɗe wuta amma jajirtattun sojojin suka maida martani aka yi ɗauki ba daɗi.

Ya ƙara da cewa Jami'an tsaro sun yi nasarar tura yan ta'adda Shida lahira kuma suka kame wasu da dama, sannan suka kwace makaman su, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Makama ya ce:

"Sun damƙe gomman mayaƙan Boko Haram da suka haɗa da masu samar musu da kayan aiki, masu haɗa kai da su, kana kuma suka kwato makamai da dama."

Kara karanta wannan

Jirgin Yakin NAF Ya Yi Luguden Bama-Bamai Kan Mafakar Shugaban Yan Ta'adda a Sambisa

Me ake yi a kasuwar?

Rahoto ya nuna cewa masu kasuwanci a wurin suna sayar da abubuwa kamar Masara, Wake, Gishiri Maggi, Tufafin da aka taɓa amfani da su, Kwayoyi da Man Fetur ga ƴan ta'adda domin musaya da ɗanyen ƙarfe.

Legit.ng Hausa ta gano cewa yanzu haka an kai waɗanda suka shiga hannu Hedkwatar Rundunar Amoured Brigade da ke garin Bama domin cigaba da bincike.

A wani labarin kuma Sojoji Sun Hallaka Ƙasurguman Yan Ta'adda da Yawa a Yankuna Uku Na Arewa

Shugaban hukumar sojin saman Najeriya, Oladayo Amao, ya ce haɗin kan hukumomin tsaro ya haifar da gagarumar nasara.

A cewarsa, samamen da sojoji suka kai mafakar yan ta'adda ta sama da ƙasa a shiyyoyin arewa uku ya halaka manyan yan tada ƙayar baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel