Osinbajo, Lawan, Da Sauran Mutum 20 Da Suka Sayi Fom Din APC Zasu Gana Don Tinubu

Osinbajo, Lawan, Da Sauran Mutum 20 Da Suka Sayi Fom Din APC Zasu Gana Don Tinubu

  • Jam'iyyar APC zata tara dukkan yan takara a zaben fidda gwani don hada kai wajen ganin Tinubu ya ci zabe
  • Tinubu ya lallasa wadannan yan takara a zaben fidda gwanin APC yayinda ya samu kuri'u 1,271
  • Hukumar INEC zata gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya ranar 28 ga Febrairu, 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Mutum 22 da sukayi Fom din N100m na takara a zaben fidda gwanin shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zasu gana don hada kai wa dan takara, Asiwaju Bola Tinubu.

TheNation ta ruwaito cewa an shirya wannan zama ta musamman ranar Laraba mai zuwa don tattauna yadda Tinubu zai lashe zaben 2023.

Wannan shawara ya biyo bayan kaddamar da ofishin kamfen Tinubu da Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, yayi a Damataru.

Daya daga cikin yan takaran a jawabin da ofishin yada labaransa ya fitar, yace za'a yi wannan zama ne a Abuja.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Nuna Yadda Za a Raba Ayyuka Muddin Tinubu Ya Hau Mulki

A cewar jawabin:

"Wannan gayyata ta musamman zuwa zaman dukkan yan takaran shugaban kasa na APC wanda za'ayi a Transcorp Hilton Abuja, ranar Laraba, 31 ga Agusta 2022 misalin karfe 2, za'a tattauna hanyoyin yakin neman zaben da za'a bi wajen hada kan kowa don magance matsalolin kasarmu."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

APC Primary
Osinbajo, Lawan, Da Sauran Mutum 20 Da Suka Sayi Fom Din APC Zasu Gana Don Tinubu
Asali: Facebook

Wadanda ake sa ran zasu halarci zaman sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, tsohon Ministan Kimiya Ognonnaya Onu, tsohon karamin ministan Ilimi Emeka Nwajuiba da tsohon ministan Neja Delta, Godswill Akpabio.

Hakazalika akwai gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, gwamnan Ebonyi Dave Umahi, gwamnan Jigawa Abubakar Badaru, gwamnan Cross River Ben ayade, gwamnan Ekiti Kayode Fayemi da tsohon gwamnan Zamfara Ahmad Sani Yarima.

Sauran sune Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, Sanata Ibikunle Amosun, Sanata Ajayi Borrofice, tsohon Kakakin majalisa Dimeji Bankole, Fasto Tunde Bakare, Fasto Nicholas Felix, Ikeobasi Mokelu, Tein Jack-Rich da Mrs Uju Ken-Ohanenye.

Kara karanta wannan

Magidanci Mai Mata 4 Da 'Yaya 34 Sun yi Rijistan Zabe, Yace Atiku Duk Zasu Kadawa Kuri'u

Zaku tuna cewa Tinubu ya lallasa wadannan yan takara a zaben fidda gwanin APC yayinda ya samu kuri'u 1,271.

Wanda ya zo na biyu shine Amaechi wanda ya samu kuri'u 316, sannan Osinbajo mai kuri'u 235.

Kashim Shettima Ya Nuna Yadda Za a Raba Ayyuka Muddin Tinubu Ya Hau Mulki

A wani labarin kuwa, Kashim Shettima wanda shi ne ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa a APC, yace zai maida hankali ga tsaro idan suka kafa gwamnati.

Premium Times tace Sanata Kashim Shettima ya sha alwashin idan suka yi nasara a zaben 2023, zai kula da sha’anin tsaro domin kawo zaman lafiya.

Tsohon gwamnan na Borno ya bayyana wannan a wajen babban taron NBA na kasa da aka yi a Legas, inda ya gabatar da jawabi a gaban Lauyoyi.

Shettima ya fadawa mahalarta zaman da aka yi a farkon makon nan cewa jagoranci jami’an tsaro wajen ganin an samu zaman lafiya a Najeriya

Kara karanta wannan

Mu ba butulu bane: Tinubu ne zan gaji Buhari a 2023, Insha Allahu, Masari ya bayyana dalilai

Asali: Legit.ng

Online view pixel