Bidiyo: Magidanci Ya Ki Karbar Nama Yanka 2 Da Matarsa Ta Bashi, Ya Shiga Madafi Ya Diba Da Kansa

Bidiyo: Magidanci Ya Ki Karbar Nama Yanka 2 Da Matarsa Ta Bashi, Ya Shiga Madafi Ya Diba Da Kansa

  • An gano bidiyon wani magidanci dan Najeriya a Twitter yana korafi tare da yiwa matarsa fada kan bashi yankan nama biyu kacal a abinci
  • Mutumin ya ce baya jin dadin yadda matarsa ke aikata hakan a kodayaushe duk da cewar shine yake fita nemo kudin da aike amfani da shi a gida
  • Daga nan sai fusataccen mijin ya shiga madafi da kansa ya dibi isasshen shinkafa da miya sannan ya daura nama manyan yanka har guda hudu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya – Bidiyon wani magidanci yana yiwa matarsa korafi a kan basa yankan nama biyu kacal a kodayaushe ya baiwa mutane da dama dariya sannan ya haifar da martani sosai a soshiyal midiya.

A cikin bidiyon wanda shafin @instablog9ja ya wallafa a Twitter, mutumin ya bayyana cewa shine yake fita samo kudaden da ake kashewa don haka ya cancanci ayi masa karin nama a abinci.

Kara karanta wannan

Ya Rabu Dani Saboda Ina Da Muni: Hotunan Sauyawar Wata Budurwa Shekaru Bayan Saurayi Ya Guje Ta Ya Ba Da Mamaki

Magidanci
Bidiyo: Magidanci Ya Ki Karbar Nama Yanka 2 Da Matarsa Ta Bashi, Ya Shiga Madafi Ya Diba Da Kansa Hoto: @instablog9ja.
Asali: Instagram

Mutumin wanda ya fusata matuka ya tsawatarwa matarsa sosai yayin da ya shiga madafi da kansa sannan ya zubawa kansa abinci da hannunsa ba tare da bata lokaci ba.

Ya diba shinkafa isasshe da miya sannan ya dauki nama manyan yanka guda hudu. Bidiyon ya haifar da martani masu ban dariya sosai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

@blessedamao ya ce:

“Nima na lura idan bana nan, sai su cikawa kansu nama da kaji. Idan na dawo, sai a bani dan kadan. Don haka na yanke shawarar fita a kodayaushe na ci dukka ASUN, Shawarma da talo-talo duk daren Juma’a da Asabar.

@za__rah ta ce:

“Me ya hada maza da nama ne? kalli yadda yake korafi kamar wani shagwababbe. Sauran mutane na za su ci naman ba? Ya ma ci sa’a ya samu yanka biyu.”

Kara karanta wannan

“Zan Iya Hada miliyan N10 Duk Wata”: Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ke Mayar Da Sharar Robobi Su Zama Bulo

@Peaghy ya yi martani:

“Wannan abun ko.. Nima na so yiwa matata korafi..tukunyar miya da ke da talo-talo da kaji da katantanwa, ina nufin isasshen katantanwa fa, sai a kawo mun 2 wasu lokutan 1 duk dare, amma duk lokacin da nake son yin korafi sai na tuna kalmar mahaifiyata “nama baya kosar da mutum.”

Yadda Jami’an Yan Sanda Suka Je Har Wajen Shagalin Biki Suka Kama Amarya Kan Zargin Sata

A wani labari na daban, an tashi zuru-zuru a wajen wani liyafar aure bayan jami’an yan sanda sun farmaki wajen taron sannan suka kama amaryar a kan zargin sata.

Shafin LIB ya rahoto cewa na tsaka da gudanar da bikin ne a ranar Asabar, 20 ga watan Agusta, a makarantar Kimiyya ta Kakiika da ke birnin Mbarara, Uganda, lokacin da jami’an tsaron suka zo suka tafi da amaryar Ms. Christine Natuhera sannan suka garkame ta.

Kara karanta wannan

Sabon Shiga: Bidiyon Yadda Matashi Ya Zunduma Ihu Cike Da Tsoro Bayan Ya Shiga Jirgin Sama A Karon Farko

Manajan wajen da ta yiwa aiki mai suna Mirembe Henry, ya zarge ta da yiwa kamfanin sata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel