Sabon Shiga: Bidiyon Yadda Matashi Ya Zunduma Ihu Cike Da Tsoro Bayan Ya Shiga Jirgin Sama A Karon Farko

Sabon Shiga: Bidiyon Yadda Matashi Ya Zunduma Ihu Cike Da Tsoro Bayan Ya Shiga Jirgin Sama A Karon Farko

  • Bidiyon wani matashi ya yadu a shafukan soshiyal midiya bayan ya shiga jirgin sama a karon farko
  • A cikin bidiyon, an gano matashin ya cika da tsoro yayin da jirgin ya lulka sama, kuma hakan ya sa mutane sun yi masa dariya
  • Da suke martani ga bidiyon, wasu mabiya soshiyal midiya sun bayyana halin da suka shiga bayan sun shiga jirgin sama

Wani bidiyo mai ban dariya na wani matashi bakin fata da ya shiga jirgin sama a karon farko ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu.

A cikin bidiyon wanda ya yadu a soshiyal midiya, an gano matashin yana jan numfashi sannan ya kurma ihu yayin da jirgin saman ya lula iska.

Matashi da jirgin sama
Sabon Shiga: Bidiyon Yadda Matashi Ya Zunduma Ihu Cike Da Tsoro Bayan Ya Shiga Jirgin Sama A Karon Farko Hoto: @bcrworldwide / Craig Hastings
Asali: Instagram

Wani mutum da ya cika da mamaki ya zauna kusa dashi sannan ya nadi bidiyonsa yayin da yake dariya ba kakkautawa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wasu Yan Mata Biyu Suka Ba Hammata Iska A Wajen Cin Abinci Saboda Wani Alajin Birni

Bayan ya lura cewa yana haifar da yar dirama da yanayinsa mai ban al’ajabi, sai ya yi dariya sannan ya kama kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon wanda @bcrworldwide ya wallafa a kasa:

Jama’a sun yi martani a kan bidiyon

Bidiyon da ya yadu ya sanya mutane tofa albarkacin bakunansu.

Jare_ahmed ya ce:

“Na tuna ranar da na fara shiga jirgi. Wannan gayen bai kaini ba. Abun ba sauki. Ji nayi kamar zan mutu a wannan ranar.”

Preshemirate ta ce:

“Ba sabon shiga ba kawai, kullun haka nake.”

Big_baby_anita ta ce:

“Hakan na nufin cewa duk ranar da zan shiga jirgi zan sha wauta har na gaji.”

Kingquojo ya yi martani:

“Mutumina ya ji tsoro.”

Kudi Kare Magana: Bidiyon Katafaren Gida Da Wani Matashi Ya Kera Cikin Watanni 4

A wani labarin, wani matashi dan Najeriya ya je shafin soshiyal midiya don murnar kammala ginin gidansa na biyu a cikin watanni 4.

Kara karanta wannan

Kamar almara: Sauyawar wani matashi daga sana'ar acaba zuwa tauraro ya ba da mamaki

Matashin wanda ke amfani da shafin @kelvinwhite12 a TikTok ya wallafa wani bidiyo da ke dauke da yadda aka fara aikin gidan da kammala shi.

Shafin farko ya nuna lokacin da aka fara ginshikin gidan da masu aikin gini suna ta aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel