Jirgin Soji Ya Saki Ruwan Bama-Bamai A Mafakar Shugaban Yan Ta'adda a Dajin Sambisa

Jirgin Soji Ya Saki Ruwan Bama-Bamai A Mafakar Shugaban Yan Ta'adda a Dajin Sambisa

  • Jirgin yakin rundunar sojin saman Najeriya ya kai farmaki maɓoyar shugaban yan ta'adda, Fiya Ba Yuram, a dajin Sambisa
  • Bayanai sun tabbatar da cewa ruwan bama-baman jirgin ya hallaka dandazon yan ta'adda da ke aiki a Dajin
  • Jami'an tsaro na cigaba da samun nasara a yakin da suke da yan ta'adda a sassan Najeriya a ƴan makonnin nan

Borno - Dakarun rundunar Sojin saman Najeriya (NAF) sun yi ruwan bama-bamai kan mafakar shugaban ƙungiyar ISWAP, Fiya Ba Yuram, a dajin Sambisa da jiragen yaƙi.

Harin jirgin yaƙin wanda aka kai da nufin wasu abun hari a dazukan Tunbans da Sambisa ya hallaka dandazon yan ta'adda da ke aiki a mafakar shugaban su, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Luguden Wuta: Sojoji Sun Hallaka Ƙasurguman Yan Ta'adda da Yawa a Yankuna Uku Na Arewa

Jirgin yaƙin NAF.
Jirgin Soji Ya Saki Ruwan Bama-Bamai A Mafakar Shugaban Yan Ta'adda a Dajin Sambisa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Jaaridar Daily Trust ta tattaro cewa Fiya Ba Yuram, shi ne ya gaji kujerar tsohon shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, bayan kungiyar da ta ɓalle ta kashe shi.

Kakakin rundunar NAF, Edward Gabkwet, ya tabbatar da cigaban a wata hira da manema labarai a Abuja, inda ya ce, "A halin yanzun NAF ba zata bayyana bayanan waɗan da ta kashe ba."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ɗaya daga cikin jami'an da suka kai samamen ya bayyana cewa:

"Dakarun Sojoji da sauran hukumomin tsaro na cigaba da aikin haɗin guiwa ta hanyar amfani da ƙarfin su wajen tabbatar da an kawar da yan ta'adda, masu ta da ƙayar baya da sauran masu aikata muggan laifuka daga doron ƙasa."
Jirgin yaƙin NAF na taka muhimmiyar rawa a yakin da ake yi a sassan ƙasar nan. A jiya, jirgin NAF karkashin Operation Haɗin Kai ya kai samame maɓoyar ƴan ta'adda a dajin Sambisa da Tunbans a jihar Borno kuma an sami gagarumar naasara."

Kara karanta wannan

Zan Yanke Hukunci Kan Ko Zan Fice Daga Jam'iyyar Kwankwaso A Wannan Makon, Shekarau Ya Magantu

"Bayan samun bayanan sirri, an tura jirgin yaƙi zuwa wani wuri a dajin Sambisa da ake zaton mafakar kasurgumin ɗan ta'adda, Fiya Ba Yuram ne. Wannan jagoran yan ta'addan shi ne shugaban dajin Sambisa da ya gaji Shekau."

Ya ƙara da cewa daga isa wurin, an gano cewa wurin ya kunshi dandazon yan ta'adda, daga nan jirgin ya saki ruwan bama-bamai.

"Binciken da ka yi a wurin bayan samamen ya nuna cewa an yi gagarumar nasara, dai dai babu tabbacin ko Fiya Ba Yuram na cikin yan ta'addan da luguden ya tura barzahu."

Yan sanda sun kai hari sansanin ƴan ta'adda a Katsina

A wani labarin kuma 'Yan Sanda Sun Kai Samame Sansanin Yan Bindiga a Katsina, Sun Sheke Dan Ta'aadda

Dakarun yan sanda sun kai samame sansanin yan bindiga a kauyen Anguwan Mai Zuma, ƙaramar hukumar Ɗanja a Katsina.

Rundunar yan sanda ta ce yayin samamen, Jami'ai sun sheke ɗan ta'adda ɗaya, sun kwato kayan aikin su da yawa.

Kara karanta wannan

Har Yanzun Akwai Sauran Fasinjojin Jirgin Ƙasa a Hannun Yan Ta'adda, Mamu Ya Faɗi Mummunan Halin Da Suke Ciki

Asali: Legit.ng

Online view pixel