Sojoji Sun Hallaka Manyan Hatsabiban Yan Ta'adda da Dama a Yankuna Uku Na Arewa

Sojoji Sun Hallaka Manyan Hatsabiban Yan Ta'adda da Dama a Yankuna Uku Na Arewa

  • Shugaban hukumar sojin saman Najeriya, Oladayo Amao, ya ce haɗin kan hukumomin tsaro ya haifar da gagarumar nasara
  • A cewarsa, samamen da sojoji suka kai mafakar yan ta'adda ta sama da ƙasa a shiyyoyin arewa uku ya halaka manyan yan tada ƙayar baya
  • A kwanan nan dai, Sojoji sun yi ikirarin kashe manyan kwamandojin Boko Haram, da wasu hatsabiban yan bindiga

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun kashe manyan ƙasurguman yan ta'adda da dama a shiyyoyin arewa maso gabas, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

Hafsan rundunar sojojin sama, NAF, Air Marshal Oladayo Amao, shi ne ya yi wannan furucin ranar Talata a wurin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja.

Hafsan Sojin Sama, Oladayo Amao.
Sojoji Sun Hallaka Manyan Hatsabiban Yan Ta'adda da Dama a Yankuna Uku Na Arewa Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Hafsan sojin ya ce ƙara matsa kaimi da zafafa kai samame ta sama da ƙasa ya soma haifar da ɗa mai ido saboda danƙon haɗin kan da aka samu tsakanin hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

An Kuma: 'Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa da Matafiya da Dama a Jihar Arewa

Mista Amao, ya samu wakilcin Daraktan hulɗa da jama'a na rundunar sojin sama, Air Commodore Edward Gabwet, a wurin taron na masu ruwa da tsaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar wayar da kai ta ƙasa, (NOA), ita ce ta shirya taron a babban birnin tarayya Abuja. A kalamansa ta bakin wakilinsa, Amao ya ce:

"Mun yi amanna cewa danƙon haɗin kan da ake samu da abokanan aiki na kusa da sauran hukumomin tsaro zai taimaka matuƙa gaya wajen magance barazanar tsaro da ya addabi ƙasar nan."
"Waɗan nan kokarin aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro, babu shakka ya haifar da sakamako fiye da yadda ake tsammani."
"Da yawan shugabannin yan ta'adda sun mutu a ruwan wutan jiragen sojin sama da kuma samamen da sojojin ƙasa ke bin su da shi a ƴan makonnin na da suka gabata a arewa maso gabas, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya."

Kara karanta wannan

Har Yanzun Akwai Sauran Fasinjojin Jirgin Ƙasa a Hannun Yan Ta'adda, Mamu Ya Faɗi Mummunan Halin Da Suke Ciki

Nasarorin da Sojojin suka samu

A wata sanarwa da aka fitar a shafin FG na Tuwita, am jero dumbin nasarorin da hukumomin tsaro suka samu tsawon wata ɗaya, daga tsakiyar watan Yuli zuwa tsakiyar watan Agusta.

Sanarwan ta bayyana yadda dakaru suka kai samame mafakar yan ta'adda a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya da kuma kasurguman yan ta'addan da suka kashe.

NAF ta kara danƙon alakarta da fararen hula

Ya ƙara da cewa NAF ta gudanar da tallafin lafiya a dukkan sassan Najeriya da zummar ƙara yauƙaƙa alaƙar fararen hula da sojoji a yankunan da suke sansani.

"Kusan yan Najeriya 400,000 ne suka amfana daga shirin," a cewar Hafsan rundunar sojin NAF.

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Tattara Matafiya, Sun Yi Awon Gaba da Su a Jihar Arewa

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya shida yayin da suke kan hanyar komawa gida a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Duk wanda aka gani a harbe: Gwamnatin Zamfara ta haramta hawa babura a wasu yankuna

Hukumar yan sanda reshen jihar tace dakarunta sun yi nasarar ceto mutum huɗu daga ciki, kuma zasu kubutar da ragowar su kame maharan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel