Buhari Ya Fusata, Ya Bada Umurnin Abin Da Za A Yi Wa Sojan Da Ya Kashe Sheikh Goni Aisami

Buhari Ya Fusata, Ya Bada Umurnin Abin Da Za A Yi Wa Sojan Da Ya Kashe Sheikh Goni Aisami

  • Shugaban Najeriya Muhammadu ya nuna fushinsa game da kisar gillar da aka yi wa shaihin malami Sheikh Goni Aisami a Jihar Yobe
  • Buhari, cikin sanarwar da kakakinsa Garba Shehu ya fitar ya yi Allah-wadai da kisan ya kuma umurci rundunar sojoji ta gaggauta hukunta wanda aka samu da laifi
  • Babban hafsan tsaron na Najeriya ya kuma bukaci rundunar ta sojoji ta yi bincike ta gaggauta fatattakar bata gari daga cikinsu don kiyayye kimar rundunar

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci mahukunta a rundunar sojojin Najeriya su fatattaki bata gari daga cikinsu da ka iya aikata laifuka, Vanguard ta rahoto.

Shugaban kasar ya bada umurnin ne cikin sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar yayin martani kan kisar gillar da aka yi wa malamin addinin musulunci na Jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Buhari ya yi Allah wadai da kisan gillan da aka yiwa Shehin Malami a Yobe

Buhari
Buhari: A Gaggauta Hukunta Sojan Da Ya Kashe Sheikh Goni Aisami. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

Wasu bata garin soja da malamin ya rage wa hanya ne ya kashe shi kamar yadda yan sanda suka tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin Buhari kan kisar Sheikh Goni

Da ya ke martani kan lamarin a ranar Talata, Buhari ya yi Allah-wadai da kisar da aka yi wa malamin addinin musuluncin haka siddan, yana cewa:

"Wannan kisar gillar da aka yi wa mutum mai tausaya bayan ya yi taimako ba shi da hurumi a koyar mu na sojoji.
"Ya saba wa tarbiyyar sojoji na kamun kai da mutunta rayukan mutane da ba su ji ba ba su gani ba.
"A matsayina na babban kwamandan hafsoshi, zaluncin da jami'in tsaro da aka horas da kare rai ya aikata ya fusata ni.
"Bisa horaswar mu, an hane mu da aikata irin wannan mummunan laifin. Ba a koyar da mu jefa rayuwar farin hula cikin hatsari ba.

Kara karanta wannan

Alhassan Doguwa: Matsalar tsaro ba laifin Buhari bane, ya ma kare 'yan Najeriya ne

"Duk da cewa sojan shi kadai ya aikata wannan mummunan abin, yana iya shafa wa rundunar sojojin mu bakin fenti.
"Wannan na iya saka sauran mazauna kasar mu jin tsoron taimakawa sojoji, hakan kuma ya datse aminci da ke tsakanin sojoji da mazauna kasar."

Don haka, ina kira ga mahukunta a rundunar soji su hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan laifin ba tare da bata lokaci ba sannan su fattaki duk wasu irin wannan halin.

Ya kuma mika ta'aziyyarsa ga gwamnatin jihar Yobe, al'ummar jihar da iyalan mammacin da aka kashe.

An Kama Sojoji 2 Kan Laifin Kashe Babban Malamin Islama, Sheikh Goni Aisami, Tare Da Sace Motarsa A Yobe

Tunda farko, Rundunar yan sandan Najeriya a Yobe ta kama sojoji da ake zargi da hannu a kisar fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Goni Aisami wanda aka kashe ranar Juma'a misalin ƙarfe 9 na dare a hanyarsa ta komawa Gashua daga Kano.

Majiyoyi da dama daga garin sunyi zargin cewa sojojin sun kashe malamin ne bayan ya rage musu hanya daga shingen sojoji a Nguru zuwa Jaji-maji, wani gari da ke karamar hukumar Karasuwa na Jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel