Buhari Ya Yi Matukar Kokari Wajen Kare ’Yan Najeriya Da Dukiyoyinsu, Inji Alhassan Doguwa

Buhari Ya Yi Matukar Kokari Wajen Kare ’Yan Najeriya Da Dukiyoyinsu, Inji Alhassan Doguwa

  • Dan majalisar wakilai na Najeriya ya bayyana irin kokarin da shugaba Buhari ya yi a fannin da ya shafi tsaro
  • Alhassan Ado Doguwa ya karbi lambar yabo daga al'ummar jihar Kano a matsayin dan majalisar da ya ba da gudunmawa a harkar tsaro
  • Jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya na yawan fama da hare-haren 'yan bindiga, musamman a shekarun baya-bayan nan

Jihar Kano - Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya yaba da irin kokarin da shugaba Buhari ya yi na kare 'yan Najeriya da dukiyoyinsu.

Doguwa ya dage cewa, tsaro aiki ne na kowa, kuma shugaba Buhari ya yi iyakar kokarinsa wajen ganin bai gaza kare 'yan kasarsa ba.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi 22 ga watan Agusta a jihar Kano yayin wani taron karrama shi.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna Yuguda: Duk mai hankali da tunani ya san Buhari ya yi kokari a mulkin Najeriya

Buhari ya yi kokari wajen kare rayukan 'yan Najeriya, inji jigon APC
Buhari Ya Yi Matukar Kokari Wajen Kare ’Yan Najeriya, Inji Alhassan Doguwa | Hoo: thecable.ng
Asali: UGC

Rahoton jaridar TheCable ya ce, an karrama Doguwa ne a matsayin dan majalisar da ya tsaya, tsayin daka a fannin da ya shafi lamurran tsaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kada ku daura laifi kan Buhari, tsaro aikin kowa ne

Da yake karin haske game da matsalar da Najeriya ke ciki, jaridar Punch ta ruwaito Doguwa na cewa, bai kamata 'yan Najeriya su daura laifin masalar tsaro ga shugaba Buhari kadai ba.

Ya kuma kalubalanci 'yan kasar kowa ya kawo nasa gudunmawa wajen magance masalar tsaro, tare da cewa tunda kowa na alfahari da kasancewa dan Najeriya, to tsaro aiki ne na kowa.

Hakazalika, ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar gwamnonin Najeriya su ci gaba da irin kokarin da suke na tallafawa baun tsaro.

A bangare guda, ya yabawa malamai a Najeriya bisa kokarin da suke a fannin lamarin tsaro, haka nan ga sarakunan gargajiya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Ni tsohon ministan tsaro ne, ni zan iya gyara matsalar tsaron Najeriya

Ina son yan Najeriya suce na yi iyakan kokari na, Shugaba Muhammadu Buhari

A wani labarin, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yiwa yan Najeriya iyakan kokarinsa kuma yana sa ran idan ya sauka daga mulki zasu fadi hakan da kansu.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayin hirarsa a gidan talabijin na NTA da aka haska ranar Alhamis.

Buhari yace: "Abinda nike sa ran yan Najeriya suce shine mutumin nan ya yi iyakan kokarinsa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel