Ku Kama Ni: Hotunan Kyawawan Yan Gida Daya Da Ke Aikin Yan Sanda Ya Gigita Samari

Ku Kama Ni: Hotunan Kyawawan Yan Gida Daya Da Ke Aikin Yan Sanda Ya Gigita Samari

  • Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanan hotunan wasu yan gida daya da ke aiki a rundunar yan sandan Najeriya
  • Daya daga cikin yan matan ta wallafa kyawawan hotuna yayin da ta tuna da yayarta, wacce ga dukkan alamu ta je tafiya
  • Masu amfani da soshiyal midiya da dama sun yaba kyawun da Allah ya yi masu, maza da dama sun mato a kansu

Najeriya - Wasu kyawawan yan mata yan gida daya wadanda ke aiki a matsayin jami’an yan sandan Najeriya sun yi fice bayan hadaddun hotunansu sun yadu a soshiyal midiya.

Karamar cikinsu ta je shafin TikTok don wallafa hotunan da suka dauka tare da yayar tata kala-kala, inda ta bayyana cewa tana matukar kewarta.

Kyawawan yan sanda
Ku Kama Ni: Hotunan Kyawawan Yan Gida Daya Da Ke Aikin Yan Sanda Ya Gigita Samari Hoto: TikTok/@kuvana_of_Lagos
Asali: UGC

Hoton farko da ta daura ya nuno wasu kyawawan yan mata tsaye a gaban ofishin yan sanda cikin shigar yan sanda ta bakin kaya.

Kara karanta wannan

Hotunan Kafin Aure Na Kyakkyawar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero Da Angonta Amir Kibiya

A wani hoton kuma, yan matan sun saka ‘kayan shan iska’ yayin da suke shakatawa a bakin ruwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A dukka hotunan da ta wallafa, kyawun surar yan matan shine abun da ya ja hankali, harma ya zautar da yan maza inda suka kasa boye zalamarsu.

Kalli bidiyon a kasa:

Maza sun yaba kyawun su

Jack Sparrow⚓️ 1️⃣0️⃣1️⃣ ya ce:

"Wayyo Yesu!!! Abun ya burge ni!!!.. Ban taba sha’awar jami’ar yar sanda mace ba a baya…kashh!wannan ita ce Kalmar Haduwa!!”

Emmanuel SO Okenmuo ya ce:

“Me yasa yan sandanmu ba za su dunga kasancewa haka ba…idan ta ce yan sanda abokanku ne kawai yarda zan yi nan take….masoyiya ki garkame ni.”

Brave ya ce:

“Zan so shan mari daya daga wajenku na san cewa marin zai yi taushi a kunne.”

Kara karanta wannan

Matar Da Ta Haifi Yan 4 Ta Wallafa Kyawawan Hotunan Lokacin Da Take Goyon Ciki

User ya ce:

“Watakila zan duba yiwuwar shiga aikin yan sandan Najeriya fa, tunda rundunar sojojin Najeriya na da wahalar shiga.”

Hoton Yarinya ‘Yar Shekara 5 Dake Burin Zama Jami’ar Yan Sanda, Yan Najeriya Sun Yi Martani

A wani labarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Abuja, Prince Olumuyiwa Adejobi, ya wallafa hotunan wata karamar yarinya, Lawal Mazeedatul Khair Adesuwa, wacce ke son zama yar sanda a rayuwarta.

Olumuyiwa ya bayyana cewa yarinyar na 'Nursery 2'. Ya yi alkawarin sanya idanu a kan ci gaban Adesuwa yayin da yake mata fatan alkhairi.

Yarinyar mai shekaru 5 ta yi shiga irin na yar sanda a wani taro da suka yi a makarantansu inda kowani dalibi ya sanya kaya irin na abun da yake burin zama a rayuwa. An bayyana ta a matsayin yarinya mai kwazo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel