Na Hadu Da Shi Bai Da Ko Waya: Budurwa Ta Kasance Da Saurayinta Har Ya Siya Motar Benz

Na Hadu Da Shi Bai Da Ko Waya: Budurwa Ta Kasance Da Saurayinta Har Ya Siya Motar Benz

  • Wata matashiyar budurwa ta sha ruwan yabo bayan ta wallafa tsohon hoton saurayinta a lokacin da suka fara soyayya
  • Kyakkyawar budurwar ta bayyana cewa ta fara soyayya da shi lokacin baida ko wayar hannu
  • Mutane da dama da suka ga sauyawar da mutumin yayi sun bayyana cewa samun mata irinta abu ne mai wuya

Najeriya – Wata matashiyar budurwa @barbie_lucienne ta wallafa wani bidiyo da ke nuna saurayinta da ta kasance tare da shi lokacin da bai da komai.

Budurwar ta bayyana cewa a lokacin da ta fara soyayya da shi, mutumin bai da koda wayar hannu. Ya kasance talakan talak.

Saurayi da budurwa
Na Hadu Da Shi Bai Da Ko Waya: Budurwa Ta Kasance Da Saurayinta Har Ya Siya Motar Benz Hoto: TikTok/@barbie_lucienne
Asali: UGC

Ta kasance mai biyayya

Bayan bidiyon ya fara tafiya, sai aka gano su tare a cikin wata dankareriyar mota kirar Mercedes Benz yayin da suka rike hannayen junansu cike da so da kauna.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Hana Mahaifiyarsa Shiga Gida Saboda Yanayin Shigarta, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon sun jinjina ma biyayyarta na kasancewa da mutumin a lokacin da abubuwa ke wuya ba kamar yadda suke ba a yanzu.

Kalli bidiyon a kasa:

A daidai lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya tara martani fiye da 200 da ‘likes’ fiye da 13,000.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

First_Lady ta ce:

“Duk da haka ba duka maza ne ke kasancewa da macen da ta sha fama da shi ba. Ku yi addu’an samun mutum nagari.”

Gudboi Lëgēnd ya ce:

“Yan mata irin ki suna da wahalar samu.”

Leilathechef ta ce:

“Mace mai hakuri za ta samu komai…”

IMII ya ce:

“Haka Allah ke aikinsa.”

Qwesi Pagez ta ce:

“Wannan ya yi kyau sosai. Allah ya albarkaci wannan tarayya.”

Kara karanta wannan

Kamar almara: Sauyawar wani matashi daga sana'ar acaba zuwa tauraro ya ba da mamaki

Tirkashi: Karamin Yaro Mai Wasan Barkwanci Ya Gwangwaje Mahaifinsa Da Dalleliya Mota Sabuwa, Bidiyon Ya Yadu

A wani labarin, shahararren yaron nan mai wasan barkwanci, Kiriku, da dan uwansa sun nunawa mahaifinsu kauna inda suka siya masa sabuwar mota. Mutumin ya cika da farin ciki kan haka.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na TikTok, yaron da dan uwansa sun yi hotuna a cikin motar. A farkon bidiyon, an gano Kiriku rike da makulin motar fuskarsa dauke da farin ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel