Bidiyo: Yan Najeriya Sun Hadawa Matashin Da Ya Yi Shekaru 12 A Kurkuku Kudi Don Ya Fara Sana’ar Wanki Da Guga

Bidiyo: Yan Najeriya Sun Hadawa Matashin Da Ya Yi Shekaru 12 A Kurkuku Kudi Don Ya Fara Sana’ar Wanki Da Guga

  • Wani matashi da ya shafe tsawon shekaru 12 a gidan maza ya nuna godiyarsa bayan ya samu tallafi daga wurin mutane
  • An tattaro cewa an tura Abdul Afeez Jubril gidan yari bisa kuskure sannan ya koyi aikin wanki a lokacin da yake tsare
  • Mutanen kirki sun tallafawa matashin domin ya fara sana’ar wanki da guga na zamani bayan sun samu labarinsa mai ban tausayi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Wani matashi dan Najeriya mai suna Abdul Afeez Jubril ya nuna farin cikinsa sakamakon wani karamci da mutanen Najeriya suka nuna masa.

A cewar Alfulanny Sebilu Nnajat a Facebook, an yankewa Abdul zaman shekaru 12 a gidan yari bisa kuskure a wani shari’ar fashi da makami.

Abdul Afeez
Bidiyo: Yan Najeriya Sun Hadawa Matashin Da Ya Yi Shekaru 12 A Kurkuku Kudi Don Ya Fara Sana’ar Wanki Da Guga Hoto: Alfulanny Sebilu Nnajat
Asali: Facebook

Yayin da yake gidan yari, Abdul Afeez ya koyi yadda ake wanki da guga, kuma wannan horo ya taimaka masa bayan ya fito daga kurkuku.

Kara karanta wannan

Hotunan Kafin Aure Na Kyakkyawar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero Da Angonta Amir Kibiya

Yan Najeriya masu kirki sun samu labarinsa sannan suka hada masa tallafin kudi da zai ishi Abdul Afeez fara sana’ar wanki da guga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sebilu ya rubuta a Facebook:

“Ina godiya gareku gaba daya kan tallafawa ABDULAFEEZ JUBRIL don fara sana’ar wanki da guga da ya koya a gidan gyara hali (kurkuku), inda ya shafe tsawon shekaru 12 bisa kuskure a shari’ar fashi da makami. Dan Allah, har yanzu yana bukatar taimakonmu don hayar shago da wurin zama. Ku tura tallafinku zuwa wannan asusun: 2075440558 SEBILU NNAJAT CONCEPT UBA BANK kuma Allah ya azurta aljihunku. Ameen.”

A cikin bidiyon da aka wallafa a Facebook, an gano Abdul Afeez tsaye kusa da kayan aikinsa kuma ya yi godiya ga yan Najeriya a kan wannan wallafi da suka basa.

Jama'a sun yi martani

Semiat Agoro ta rubuta:

Kara karanta wannan

Iyayen zaman: Uba ya rufe shagon 'yarsa saboda ta ki amince a tafi da ira Italiya yawon karuwanci

"Jazakumullah kharian an gode sosai yallabai, Allah Madaukakin sarki ya ci gaba da karfafaka ta kowani hanya yallabai."

Livon Halimah ta rubuta:

"Allah ya ci gaba da karfafa ka Alhaji Al-Fulany! Jazakhumu Lahi Khaeran."

Alhaja Buliq ta ce:

"Allah ya ci gaba da karfafa ka yallabai Al fulany jazakhumu lahi kheeran."

Kalli bidiyon a kasa:

“Zan Iya Hada miliyan N10 Duk Wata”: Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ke Mayar Da Sharar Robobi Su Zama Bulo

A wani labarin, wani hazikin dan Najeriya ya ce idan har ya samu tallafi yadda ya kamata, zai dunga samun makudan kudade daga aikinsa na yin bulo.

Matashin mai kwazo wanda ake kira da suna Promise yana yin bulo masu kwari wanda ake amfani da su wajen gini da sharar robobi da aka zubar.

Sai dai a cikin wani bidiyo da ya yi, Promise ya ce a yanzu haka bashi da kudaden da zai inganta sana’arsa zuwa matakin samun riba.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Cafke Wanda Ake Zargi Yana Neman Kashe Tsohon Shugaban Majalisa

Asali: Legit.ng

Online view pixel