Bidiyon Yadda Karamar Yarinya Ta Yi Suman Karya Bayan Mahaifiyarta Ta Kama Ta Tana Fentin Bandaki

Bidiyon Yadda Karamar Yarinya Ta Yi Suman Karya Bayan Mahaifiyarta Ta Kama Ta Tana Fentin Bandaki

  • Wata karamar yarinya ta yiwa bandakinsu dan kwaskwarima ta hanyar yin zane a ciki sai kuma mahaifiyarta ta kama ta a bakin aiki
  • Bidiyon ya baiwa mutane da dama dariya yayin da yarinyar ta fadi tayi suman karya don kubutar da kanta daga abun da ta yi
  • Mutane sun sha mamakin wannan yar dirama da ta shirya sannan sun so yadda ta gaggauta kare kanta

Allah ya yiwa yara baiwa ta musamman kuma sun iya shirya makirci kala-kala don ganin tsirata da kansu a duk lokacin da suka aikata ba daidai ba.

Yara sun iya abubuwan ban mamaki da hada wuri kama daga wasan kwalliya zuwa ga wasan gyaran gashi da sauransu, kuma duk hakan na kasancewa ne a lokacin da suke tasowa da kokarin gane kan duniya.

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 16 da Aure, Magidanci Ya Fattaki Matarsa, Ya Aure Mai Gidan Haya Don Morar Hayar Kyauta

Karamar yarinya
Bidiyon Yadda Karamar Yarinya Ta Yi Suman Karya Bayan Mahaifiyarta Ta Kama Ta Tana Fentin Bandaki Hoto: Twitter / @jah_vinny_23
Asali: Twitter

A cikin irin haka ne wata yar karamar yarinya ta ga akwai bukatar yiwa bandakin gidansu kwaskwarima kwatsam sai mahaifiyarta ta kamata a kan aiki.

Wata mai amfani da shafin Twitter @jah_vinny_23 ta wallafa bidiyon karamar yarinyar wacce ta sauya bandakin gaba daya har zuwa bango da bahon bandakin, ta yiwa koina fenti da janbakin mahaifiyarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da mahaifiyar tata ta ritsa da ita, sai ta yi tunanin mafita cikin sauri kuma mafita daya gare ta shine tayi suman karya.

“Kyautar sabuwar jarumar fim mafi kwarewa ya tafi wajen….”

Kalli bidiyon kasa:

Jama’a sun yi martani

Ko shakka babu wannan yar yarinya ta iya shirya wasan kwaikwayo. Mutane sun kayatu matuka da wannan dirama da yadda ta yi wayon samawa kanta mafita.

@SmaaEvelyn ya ce:

"Ta yi kokarin kuka amma ta ga cewa ba za ta kai labari ba, kawai sai ta sume."

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Hana Mahaifiyarsa Shiga Gida Saboda Yanayin Shigarta, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

@maNtseleHlubi ta ce:

"Tana ban dariya a duk lokacin da na ga wannan. Yarinya bata bukatar tantancewa, an haifeta da shiri❤️”

@YamawelaseN ta ce:

"Bata da ko kunya, yanzu tana yi kamar ita aka cuta."

Tirkashi: Karamin Yaro Mai Wasan Barkwanci Ya Gwangwaje Mahaifinsa Da Dalleliya Mota Sabuwa, Bidiyon Ya Yadu

A wani labarin, shahararren yaron nan mai wasan barkwanci, Kiriku, da dan uwansa sun nunawa mahaifinsu kauna inda suka siya masa sabuwar mota. Mutumin ya cika da farin ciki kan haka.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na TikTok, yaron da dan uwansa sun yi hotuna a cikin motar. A farkon bidiyon, an gano Kiriku rike da makulin motar fuskarsa dauke da farin ciki.

Yan sa’anni bayan nan, sai ga mutane sun taru a wajen motar don nunawa mai wasan barkwancin kauna. An yiwa dan uwansa wanka da ruwa don nuna farin ciki.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Lakcara Ta Taya Dalibarta Rainon Jinjirinta Yayin da Take Rubuta Jarrabawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel