Tirkashi: Karamin Yaro Mai Wasan Barkwanci Ya Gwangwaje Mahaifinsa Da Dalleliya Mota Sabuwa, Bidiyon Ya Yadu

Tirkashi: Karamin Yaro Mai Wasan Barkwanci Ya Gwangwaje Mahaifinsa Da Dalleliya Mota Sabuwa, Bidiyon Ya Yadu

  • Karamin yaro mai wasan barkwanci mai suna Kiriku da dan uwansa sun sha yabo a wajen mutane bayan sun gwangwaje mahaifinsu da dalleliyar mota
  • Kiriku ya sanar da labarin siyawa mahaifin nasu mota a shafinsa na TikTok inda ya wallafa bidiyonsa rike da makullin motar
  • Yan taya murna da suka hallara a wajen sun yi masu wanka da ruwa yayin da mahaifin nasu ya cika da farin ciki

Najeriya - Shahararren yaron nan mai wasan barkwanci, Kiriku, da dan uwansa sun nunawa mahaifinsu kauna inda suka siya masa sabuwar mota. Mutumin ya cika da farin ciki kan haka.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na TikTok, yaron da dan uwansa sun yi hotuna a cikin motar. A farkon bidiyon, an gano Kiriku rike da makulin motar fuskarsa dauke da farin ciki.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Hana Mahaifiyarsa Shiga Gida Saboda Yanayin Shigarta, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Kiriku da mota
Tirkashi: Karamin Yaro Mai Wasan Barkwanci Ya Gwangwaje Mahaifinsa Da Dalleliya Mota Sabuwa, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@kirikuofficial
Asali: Instagram

Mahaifin ya yi godiya ga Allah

Yan sa’anni bayan nan, sai ga mutane sun taru a wajen motar don nunawa mai wasan barkwancin kauna. An yiwa dan uwansa wanka da ruwa don nuna farin ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A lokacin da aka hasko mahaifinsu, ya cika da farin ciki matuka. Mutumin ya duka kan gwiwowinsa tare da daga hannu don nuna godiya ga Allah.

Kalli bidiyon a kasa:

A daidai lokacin rubuto wannan rahoton, bidiyon ya tattara martani fiye da 400 da ‘likes’ fiye da 15,000.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

Jara Sam Samuel ya ce:

“Yaranka na sanya mu farin ciki.”

Akeeb Rukayat ta ce:

“Allah ya barkace ku.”

standard blessing ta ce:

“Kalli yadda suka yiwa Kiriku wanka da ruwa. Ina tayaku murna wannan ya yi.”

Kara karanta wannan

Shin tana kanne: Martanin 'yan Najeriya ga bidiyon wani matashin da ya yi wuff da baturiya

Nakuda Mai Tsada: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Dalleliyar Range Rover Saboda Ta Haifa Masa Da

A wani labarin, wata matar aure ta yi nakuda mai tsada bayan maigidanta ya siya mata dankareriyar mota kirar Range Rover 2023 a matsayin tukwicin haifa masa da na uku.

Nizi Rozay ta bayyana cewa sun yi odar tsadaddiyar motar a watan Janairu yayin da ta wallafa hadaddun hotunan dankarariyar abar hawan a shafinta na soshiyal midiya, kuma tuni suka yadu.

Ta wallafa hadaddun hotuna hudu masu sace zuciyar duk wanda ya yi arba da su dauke da rubutu kamar haka:

“A karshe na karbi tukwicin nakudata! Musamman muka yi odarta a watan Janairu kuma a karshe ta zama tawa! Sabuwar Range Rover kirar 2023."

Asali: Legit.ng

Online view pixel