Sunaye: Jihohin Kano, Zamfara da Enugu Sun yi Sabbin Kwamishinonin 'Yan Sanda

Sunaye: Jihohin Kano, Zamfara da Enugu Sun yi Sabbin Kwamishinonin 'Yan Sanda

  • Hedkwatar 'yan sandan Najeriya ta aike da sabbin kwamishinonin 'yan sandan jihohin Kano, Zamfara da Enugu
  • A takardar mai lamba TH.5361/FS/FHO/ABJ/SUB.4/715, Lawal Abubakar aka tura Kano, Yusuf Kolo yana Zamfara sai Ahmed Ammani jihar Enugu
  • Kamar yadda takardar ta bayyana, sabbin kwamishinonin 'yan sandan zasu fara aiki a take ne bayan fitar takardar

FCT, Abuja - Hedkwatar 'yan sandan Najeriya dake garin Abuja ta tura sabbin kwamishinonin 'yan sanda jihohin Kano, Zamfara da Enugu.

Kamar yadda takardar mai lamba TH.5361/FS/FHO/ABJ/SUB.4/715 ta bayyana, an tura Abubakar Lawal jihar Kano yayin da aka aike Yusuf Kolo jihar Zamfara.

Alkali Baba
Sunaye: Jihohin Kano, Zamfara da Enugu Sun yi Sabbin Kwamishinonin 'Yan Sanda. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A takardar umarnin, an bayyana cewa Ahmed Ammani ne ya zama sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Enugu.

Wadannan sabbin kwamishinonin 'yan sandan zasu fara aiki a take ne, jaridar Daily Nigerian ta rahoto hakan.

Kara karanta wannan

Babu Gwamnatin Da Ta Kai Buhari Kokari a Bangaren Gine-Gine a Tarihin Najeriya, Lai Mohammed

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sabon kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, wanda aka dauko daga jihar Enugu, a wani lokacin baya shi ne DPO din yankin Hotoro dake jihar Kano.

Tuban Turji: 'Yan Najeriya Sun yi Martani, Suna Zargin Akwai Lauje Cikin Nadi

A wani labari na daban, 'yan Najeriya sun dinga martani kan rahoton dake bayyana cewa gagararren 'dan bindiga Bello Turji, wanda ya saba kashewa da garkuwa da jama'a a Sokoto da Zamfara ya tuba.

Idan za a tuna, a watan Disamban 2021, shugaban 'yan bindigan ya rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Bello Matawalle da Sarkin Shinkafi kan yana so a tsagaita da ruwan wuta.

A yayin jawabi a wani taro a Gusau a ranar Lahadi, mataimakin gwamnan jihar, Hassan Nasiha, ya bayyana cewa Turji ya tuba kuma ya rungumi matakan zaman lafiya na gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Tuban Turji: 'Yan Najeriya Sun yi Martani, Suna Zargin Akwai Lauje Cikin Nadi

Nasiha yace Turji ya tuba kuma hakan ya dawo da zaman lafiya a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel