Gwamnatin Borno na Shirin Sake Gina Garin da Boko Haram ta Kwace a Baya
- Gwamnatin jihar Borno ta fara shirin gyara garin Gudumbali, garin da sojoji suka kwato daga hannun 'yan Boko haram kwanan nan
- Kamar yadda kwamishinan RRR, Injiniya Mustapha Gubio ya sanar, za a gyara kadarorin gwamnati tare da gidajen jama'a domin su dawo su zauna
- Ya sanar da cewa, abinda suke bukata na farko a yanzu shine saka sansanin sojoji a garin ta yadda gyaran zai zo cikin kwanciyar hankali
Borno - Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da shirinta na sake gina kadarorin gwamnati da gidaje dake tsohon madaddalar Boko Haram wacce sojoji cikin kwanakin nan suka kwato, Daily Trust ta rahoto..
Kwamishinan ma'aikata gyare-gyare da dawo da jama'a gidajensu, Injiniya Mustapha Gubio, ya sanar da hakan bayan ziyartar garin Gudumbali, hedkwatar karamar hukumar Guzamala ta jihar Borno da yayi.
A yayin kaddamar da sake mayar da 'yan gudun hijira gidajensu a watan da ya gabata, Gwamna Babagana Zulum ya yi kira ga sojoji da su sake kwato garin Gudumbali wanda hakan zai bada damar sake gina shi tare da mayar da jama'a gidajensu.
A shekarar 2014, garin Gudumbali ya fuskanci farmakin 'yan ta'addan Boko Haram a karon farko kuma dole ta sa mazauna garin suka arce zuwa Monguno da Maiduguri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A shekarar 2018, an mayar da su garin Gudumbali amma bayan wata uku tak, 'yan ta'addan sun saka fatattakarsu.
Injiniya Gubio ya jaddada cewa a yanzu da aka sake kwace garin,abunda kwamitin zai fara bai wa fifiko shine tura sojoji wurin ta yadda za a sake ginawa da gyara wurin cikin kankanin lokaci.
"Mun duba yadda yawan barnar da aka yi wa Gudumbali take. Kamar yadda shugaban kwamitin yace, za mu koma domin kai wa gwamna rahoto ta yadda za a fara gyaran garin. Bayan nan sai a fara dawo da jama'a."
A yayin bayani kan abinda zasu bai wa fifiko, "Muna bukatar jami'an tsaro a kasa, su kasance a ko ina a garin Gudumbali. Wannan zai bamu damar zuwa mu gyara garin tare da fara gyaran kadarorin gwamnati da gidajen jama'a."
Hotunan Zulum a sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi, ya bai wa masu komawa gida N.5b
A wani labari na daban, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya gwangwaje ‘yan gudun hijira fiye da mutane 5000 da rabin biliyan daya, Daily Trust ta ruwaito.
‘Yan gudun hijiran sun nuna bukatar komawa gidajensu ne don su cigaba da rayuwa. Gwamnan ya isa sansanin ‘yan gudun hijiran da misalin 5:45am inda aka fi sani da Bakassi a Maiduguri.
A takardar wacce hadimin gwamna Zulum ya saki, ya ce gwamnan ya yi sa’o’i 7 ya na jagorantar raba kudade da kayan abinci yayin da ya kai ziyarar ta ba-zata don tallafa wa mabukata da marasa gida saboda wasu mutanen su na zuwa sansanin ‘yan gudun hijiran tun safe sai dare su ke komawa gidajensu da sunan su ‘yan gudun hijira ne.
Asali: Legit.ng