Zan Mika Jami’o’in Tarayya Ga Gwamnatin Jihohi, inji dan takarar PDP Atiku

Zan Mika Jami’o’in Tarayya Ga Gwamnatin Jihohi, inji dan takarar PDP Atiku

  • Jami'o'i a Najeriya sun shafe akalla watanni shida a garkame, lamarin da ke kara dagula fannin ilimi a kasar
  • Dan takarar shugaban kasa a PDP ya bayyana aniyarsa ta mika ragamar jami'o'in gwamnatin tarayya ga gwamnatin jihohi
  • Atiku Abubakar ya halarci wani babban taro da aka gudanar a jihar Legas, inda manyan 'yan siyasa suka hallara

Jihar Legas - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai sauya akalar rikon jami’o’in gwamnatin tarayya, inda zai ba gwamnatin jihohi ragamarsu.

Atiku ya bayyana haka ne a yau Litinin 22 ga watan Agusta a bikin bude taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya na 2022 da aka gudanar a Otal din Eko and Suites da ke Legas a Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

Abin da ya muka yi a Borno da Legas zai maimaitu a kan 'yan Najeriya, inji abokin takarar Tinubu

Taron mai taken ‘Bold Transitions’ zai gudana ne har zuwa ranar 26 ga watan Agustan wannan shekarar, Channels Tv ta ruwaito.

Atiku ya bayyana yadda zai kawo karshen matsalolin jami'a a Najeriya
Zan Mika Ragamar Jami’o’in Tarayya Ga Gwamnatin Jihohi, inji dan takarar PDP Atiku | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da yake bayyana dalilinsa na kudurin mika jami'o'in Najeriya ga gwamnatocin jihohi, ya ce gwamnatin Najeriya ba ta da isassun kayan aikin ci gaba da rike jami'o'i, rahoton TheCable.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Hanya daya tak ita ce tabbatar da an samu yanayi mai kyau ga masu zuba jari na kasashen waje da na gida don zuwa kasarmu, ko fannin ababen more rayuwa, ko fannin ilimi, ko ma dai mulki ne.
“Na taba musu da malamin jami’a daga Jami’ar Tarayya ta Lokoja. Ya ce ya karanta a cikin jaddawalin kudurori na cewa na yi niyyar sauya, wato mayar da fannin ilimi ga jihohi. Ta yaya zan yi hakan?
“Na ce, ‘Malam Farfesa, shin kasan cewa rukunin farko na jami’o’inmu mallakin gwamnatocin yanki ne?’ Ya ce, ‘Eh’. Na ce to su waye magada wadannan gwamnatocin yankin? Yace jahohi ne.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Duk da Kokarin Sasanci, An Garkame Otal da Gidajen Mai na Mutanen Atiku a Ribas

“Na ce yaranku da da kuke turawa Amurka, Ingila, su waye suka mallaki wadacan jami’o’in? Da yawa mutane masu zaman kansu. To, me ya sa kake tunanin mu ba za mu iya yin hakan ba? Shin ba mu da kudin ne."

Batun yajin aikin ASUU

Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta shiga yajin aikin tun ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar, sun shafe sama da watanni shida a kasa saboda neman yadda za a gyara tsarin aiki a jami'a.

Haka nan, daliban jami'a a Najeriya nan dirshan a kasa tun bayan barkewar yajin aikin, lamarin da ya sa jama'a ke nuna damuwa ga karuwa zaman kashe wando.

A shekarar 2020 kadai, ASUU ta shiga makamancin wannan yajin aiki, inda ta shage watanni tara ba tare da zuwa makaranta ba.

Bata sauya zane ba, an sha ganin 'ya'yan shugabannin siyasan Najeriya a kasashen waje, inda suke karbar takardun kammala digiri yayin da jami'o'in kasar ke garkame.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku Da Wike: PDP Za Ta Rasa Mambobi Da Dama A Yayin Da Jerry Gana Yayi Barazanar Fita Daga Jam'iyyar

Irin Mulkin da Muka Yi a Borno da Legas, Shi Za Mu Yiwa Najeriya, Inji Abokin Takarar Tinubu

A wani labarin, abokin takarar Tinubu a zaben 2023, Kashim Shettima ya bayyana irin tagomashin da suka shiryawa 'yan Najeriya, Channels Tv ta ruwaito.

Shettima ya ce, abubuwan mamaki da Bola Tinubu ya yi jihar Legas sadda yake gwamna su ne za su kasance a Najeriya bayan 2023.

Hakazalika, ya ce za su surka da irin ababen da ya yiwa jihar Borno, domin ganin an samu ci gaba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel