Kudi Kare Magana: Bidiyon Katafaren Gida Da Wani Matashi Ya Kera Cikin Watanni 4

Kudi Kare Magana: Bidiyon Katafaren Gida Da Wani Matashi Ya Kera Cikin Watanni 4

  • Wani matashi dan Najeriya ya cika da farin ciki bayan kammala ginin gidansa cikin dan gajeren lokaci mai ban mamaki
  • Matashin ya wallafa hadadden bidiyo yayin da ya kammala katafaren gidan nasa a cikin watanni 4
  • A cewarsa, wannan shine gida na biyu da ya kerawa kansa kuma hakan ya sanya mutane tofa albarkacin bakunansu

Najeriya - Wani matashi dan Najeriya ya je shafin soshiyal midiya don murnar kammala ginin gidansa na biyu a cikin watanni 4.

Matashin wanda ke amfani da shafin @kelvinwhite12 a TikTok ya wallafa wani bidiyo da ke dauke da yadda aka fara aikin gidan da kammala shi.

Shafin farko ya nuna lokacin da aka fara ginshikin gidan da masu aikin gini suna ta aiki.

Matashi da gini
Kudi Kare Magana: Bidiyon Katafaren Gida Da Wani Matashi Ya Kera Cikin Watanni 4 Hoto: TikTok/@kelvinwhite12
Asali: UGC

A wani shafin kuma an nuno lokacin da aka kawo kayan aiki wajen kangon. An kewaye filin gidan da bulo mai kalar lemun zaki wanda yayi daidai da fetin ginin.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Karamin Yaro Mai Wasan Barkwanci Ya Gwangwaje Mahaifinsa Da Dalleliya Mota Sabuwa Fil, Bidiyon Ya Yadu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika an kashe makudan kudi a cikin gidan kama daga na’urar fitila zuwa kujeru na zamani ajin farko.

Mutumin wanda ya cika da farin ciki yace duk aikin Allah ne don shi ya shige masa gaba.

Kalli bidiyon a kasa:

Ana ta aike masa da sakonnin taya murna

Collins ya ce:

“Dan uwa Allah ya yi mun irin naka Ina so na kera gida a wannan shekarar.”

Queen B ta ce:

“Ina tayaka murna, Allah hakan ba zai yi muni ba idan nima na kera nawa gidan faaa.”

Amarachi Bethel ta ce:

“Ina taya ka murna dan uwa.
“Allah ya kara bude maka hanya amma muma ku nuna mana hanya amma kafin nan ka nuna mun kauna.”

Preshy ya ce:

“Ina taya ka murna nawa nima na hanya alfarmar za ta riskeni da mijina."

Kara karanta wannan

Kamar Akulki: Yar Najeriya Da Ke Aiki A Dubai Ta Yi Bidiyon Dakin Da Take Rayuwa Da Gadaje Irin Na Yan Makaranta

Na Hadu Da Shi Bai Da Ko Waya: Budurwa Ta Kasance Da Saurayinta Har Ya Siya Motar Benz

A wani labarin, wata matashiyar budurwa @barbie_lucienne ta wallafa wani bidiyo da ke nuna saurayinta da ta kasance tare da shi lokacin da bai da komai.

Budurwar ta bayyana cewa a lokacin da ta fara soyayya da shi, mutumin bai da koda wayar hannu. Ya kasance talakan talak.

Bayan bidiyon ya fara tafiya, sai aka gano su tare a cikin wata dankareriyar mota kirar Mercedes Benz yayin da suka rike hannayen junansu cike da so da kauna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel